Ranar 20 ga watan Afrilu ta bana rana ce da aka yi shagulgulan murnar bikin Easter a kasashen masu bin addinin Kirista, kuma yi wa kwan kaza fenti mai launuka iri-iri ta kasance daya daga cikin al’adun da ake bi a wajen bikin. Sai dai Amurkawa sun samu bambancin wannan al’adar tasu a bana, inda Amurkawa da yawa suka fara yin amfani da dankali ko kuma kwan da aka yi da roba a maimakon kwa da suka saba amfani da shi, sakamakon farashin kwai da ya yi tashin gwauron zabo da ake fuskanta a kasar.
Ashe, tun farkon shekarar da muke ciki, Amurka ta yi ta fama da matsalar karancin kwan kaza da aka samar a kasuwar gida, sakamakon annobar murar tsuntsaye da ta yadu a kasar. Duk da irin yanayin da ta samu kanta a ciki, Amurka ta sanar da kakaba wa dukkan kasashen da ke huldar ciniki da ita, ciki har da babbar kawarta kungiyar tarayyar Turai, a sa’i daya kuma, ta rubuta wa kasashen Turai wasiku don rokon su sayar mata da kwai. Babu tantama, kasashen Turai da suka hada da Denmark da Faransa da Sweden da sauransu suka amsa cewa, ba su da ragowar kwai da za su iya ba ta. Har ma a kasar Netherland, masu kiwon kaza sun ce, matukar Amurka ta cire harajin da ya kai har kaso 20% da ta kakaba musu, lallai ba za su kara fitar da kayayyakinsu ba. A yayin da take kaddamar da yakin ciniki, tana kuma rokon taimako. Matakai masu sabani da juna da Amurka ta dauka sun sanya kawayenta cikin firgici, har ma kafofin yada labarai na cikin gidanta suka yi sukar cewa “batan basira” ne.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Sin Da Birtaniya Da Su Kiyaye Tsarin Kasa Da Kasa Da Aka Kafa Bayan Yakin Duniya Na Biyu
- Gwamnatin Kano Ta Soke Tsaftar Muhalli A Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB
A hakika, abubuwa na batan basira ba su kare ba a yakin haraji da Amurka ta kaddamar a kan kasashen duniya. Misali daga cikin jerin kasashen da Amurka ta sanar da kakkaba harajin ramuwar gayya a kansu, har ma da tsibirin Heard da tsibiran McDonald, wadanda ke can kusa da Antarctic, duk da cewa babu wasu mutanen da ke zaune a wurin in ban da dabbobin da ake kira da Penguin a Turance, kuma babu harkokin shige da fice a tsakaninsu da Amurka, amma Amurka ta kakaba haraji na kaso 10% a kansu, kasancewar suna karkashin ikon kasar Australia ce. Har ila yau, Lesotho kasa ce da ke kudancin nahiyar Afirka, wadda ke daya daga cikin kasashen da suka fi fama da koma baya a duniya, duk da haka, Amurka ta sanya mata harajin fito har na kaso 50%. A cewar shugaba Trump, Lesotho na karbar harajin da ya kai kaso 99% a kan kayayyakin da ake shigar mata daga Amurka, alkaluman da gwamnatin kasar Lesotho ta ce ba ta san asalinsu ba.
Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a kan wasu kasashe na kwanaki 90. Kuma kashegari sai aka ji ya yi barazanar cewa, in dai ba a kai ga cimma daidaito a shawarwari ba, to, Amurka za ta maido da harajin. Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi gyara ta ba-zata a kan dokokinta na haraji, inda ta cire harajin ramuwar gayya a kan kayayyakin lataroni da suka hada da wayar salula da kamfuta da sauransu.
Haraji abu ne da ya shafi manufar kasa, amma ga shi gwamnatin Amurka ta mai da shi kamar wasa, wanda hakan ya bayyana rashin tunani na manufofin haraji na kasar, da ma yadda take mai da su a matsayin makamai na nuna fin karfi a duniya. Amurka ta ce wai tana neman tabbatar da yi mata adalci ne, amma a hakika kuwa, tana neman kakaba fifikonta ne a kan sauran kasashe.
Tabbatar da ci gaba hakki ne ga kowace kasa a maimakon wasu kasashe kalilan. Kasashen duniya na rungumar adalci a maimakon nuna fin karfi. Tabbas Amurka za ta cije a yunkurinta na neman tabbatar da fifikonta a kan sauran kasashen duniya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp