Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum.
Yayin da take mai da martani a kan batancin da hukumar Amurka ta yi game da harkokin da suka shafi yankunan musamman na Hong Kong da Macao na Sin, Mao Ning ta ce, tabbas ne manufar “Kasa daya, mai tsarin mulki biyu” za ta yi karko ta kuma samu ci gaba.
- Rushewar Gini Ya Kashe Rayuka 4, An Ceto Mutane 105 A Abuja A 2024 – FEMD
- Bukukuwan Kirismeti: Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Iyalan Waɗanda Suka Rasu Sakamakon Turmutsitsi A Wasu Jihohi
Dangane da barazanar da Donald Trump ya yi cewa, Amurka za ta “sake karbe” mashigin ruwa na Panama, Mao Ning ta bayyana cewa, bangaren Sin ya dade yana goyon bayan al’ummun Panama wajen kiyaye ikon mulkin mashigin ruwa na Panama cikin adalci, kuma zai ci gaba da mutunta ikon mulkin Panama kan mashigin ruwa na kasar.
Bugu da kari, Mao Ning ta ce, bangaren Sin yana goyon bayan kasashe masu tasowa wajen ba da gudummawa ga warware rikicin Ukraine.
Idan za a iya tunawa, ko a ran nan, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Wu Qian, ya bayyana cewa, Sin ta bukaci Amurka da ta daina ba da tallafin aikin soji da sayar da makamai ga yankin Taiwan, da kuma dakatar da huldar soji da yankin na Taiwan na Sin. (Safiyah Ma)