• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taimkon Juna Tushen Dangantakar Sin Da Afrika

by CMG Hausa
2 years ago
Sin

A farkon wannan mako ne shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya fara ziyarar aiki a kasar Sin, inda da yammacin jiya agogon Beijing, ya gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping.

A ranar 24 ga wannan wata ne za a cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Eritrea, wanda ke tabbatar da irin dadaddiyar huldar dake tsakaninsu.

  • Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Zai Bunkasa Ayyukan Masana’antu A Afrika

Da yake jawabi yayin ganawarsa da takwaransa na Eritrea, shugaban kasar Sin ya ce, ba tare da la’akari da yadda yanayin duniya zai kasance a nan gaba ba, mutunta juna da goyon baya da taimako, su ne za su kasance tubalin abota tsakanin Sin da Kasashen Afrika.

Idan ana batun mutunta juna, to ba shakka kasar Sin ta kasance mai mutunta ikon mulki da cikakken ’yancin kasashen Afrika, domin ta kasance kasar da ta samu ci gaba ba tare da bautar da su ko ci da guminsu ba, haka kuma ba ta yi musu katsalandan cikin harkokinsu na gida.

A ko da yaushe, kasar Sin ta kan nuna girmamawa da kwarin gwiwarta kan karfin kasashen Afrika, inda take bayyana cewa, al’ummar Afrika su suka san matsalolinsu, kuma su ne za su iya samar da mafita, wannan hali ne na dattako da sanin ya kamata. Har ila yau, ita ce mai karfafa musu gwiwar lalubo hanyoyin da suka dace da su na samun ci gaba, ba tare da arowa daga waje ba.

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Wannan ya nuna matsayinta na babbar kasa da kuma burinta na ganin sun tsaya da kafafunsu, sun samu ci gaba ba tare da dogaro da wasu bangarori da za su gindaya musu sharuda ko danne su ko kuma yi musu katsalandan ba.

Su ma a nasu bangare, mutuncin suke nunawa ta yadda suke amincewa da manufar kasancewar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan matakan tabbatar da tsaro da take dauka a cikin gida da kuma kauracewa tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida.
Taimako kuwa, ba zai misaltu ko ya kirgu ba. Ko a wannan lokaci da duniya ke fuskantar rashin tabbas da halin son kai daga manyan kasashe, kasar Sin ta tsaya kan bakanta na taimakawa kasashen Afrika.

Kama daga ababen more rayuwa, fasahohin ayyukan gona da kiwon lafiya da tsaro da cinikayya da sauransu. Kasar Sin tana bude kofarta ga kasashen Afrika domin su shigo su ci gajiyar babbar kasuwarta, haka kuma tana karfafawa kamfanoninta da masu zuba jari gwiwar shiga kasashen Afrika domin su zuba jari. A nasu bangare, kasashen Afrika sun kasance masu maraba da kayayyaki kirar kasar Sin da bude kofa ga kamfanonin da ’yan kasuwa Sinawa a kasashensu.

Nasarori da kyakkyawan tasirin dangantakar bangarorin biyu a bayyane yake, domin Sin da Afrika sun zarce abokai, sun koma ’yan uwa, su kasance masu martaba juna da cin moriyar juna da kuma neman ci gaba na bai daya, ba tare da son ganin faduwar daya daga cikinsu ba. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya Dawo Nijeriya Daga Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya Dawo Nijeriya Daga Landan

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Kaduna Za Ta Ɗauki Ma’aikatan Lafiya 9,000 Cikin Shekaru 5 – Maiyaki 

Gwamnatin Kaduna Za Ta Ɗauki Ma’aikatan Lafiya 9,000 Cikin Shekaru 5 – Maiyaki 

November 10, 2025
Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5

November 10, 2025
Matatun mai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.