Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wani mutum mai suna Amoda Bola mai shekaru 49 da haihuwa bisa zarginsa da dirka wa diyarsa mai shekaru 14 ciki
Wanda ake zargin mazaunin titin Idi Oro, Ode Remo, an kama shi ne biyo bayan korafin da diyarsa ta shigar a hedikwatar jami’an tsaro dake Ode Remo da ke karamar hukumar Remo ta Arewa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce yarinyar ta shaida wa ‘yan sanda cewa mahaifinta ya shafe tsawon shekaru yana lalata da ita.
Oyeyemi ya kuma kara da cewa, yarinyar ta ce, mahaifinta ya kuma rika gayyatar wasu maza zuwa gidan domin yin lalata da ita, daga bisani su biya shi kudi.
Kakakin ‘yan sandan ya ce bayan rahoton, DPO, Dibishin Ode Remo, CSP Olayemi Fasogbon, ya umurci jami’ansa da su taso keyar wanda ake zargin (mahaifin yarinyar).
Ya ce a lokacin da ake yi masa tambayoyi, da farko wanda ake zargin ya musanta zargin, amma daga baya ya amsa laifinsa.
Sannan kuma, ya bayyana wasu Mutum biyar da suka kwana da yarinyar a lokuta daban-daban bisa gayyatar mahaifin.
Wadanda ake zargin sune: Ahmed Ogunkoya, Dan shekara 30; Muyiwa Adeoye, Dan shekara 48; David Sunday Solaja, mai shekaru 69; Emmanuel Olusanya, mai shekaru 50; da Joshua Olaniran, mai shekaru 50.