Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar Talata a Abuja, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta kara kaimi wajen bayar da gudummawa ga fannin ilimi don ganin cewa kowane yaro dan Nijeriya, ba tare da la’akari da asalinsa ba, ya samu ingantaccen ilimi.
Da yake jawabi a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS), ya bayyana cewa, bai kamata talauci ya zama shinge ga neman ilimi ba, ya jaddada cewa, Ingantaccen ilimi ne ke yaki da talauci.
Shugaba Tinubu, wanda ya yi alkawarin yin la’akari da bukatun shugabannin kungiyar Dalibai (NANS), ya bukaci kungiyar daliban da ta tabbatar da hadin kai a tsakanin mambobinta a fadin kasar nan domin samun rabo mai tsoka.
Tun da farko, shugaban kungiyar, Umar Barambu, ya ce shugabannin NANS sun zo ne domin gode wa shugaban kasa kan rattaba hannu kan dokar lamuni na dalibai, wadda za ta tanadi rance ga dalibai marasa galihu, ta yadda babu wani dalibi dan Nijeriya a manyan makarantu da zai rasa gurbin karatunsa sabida rashin kudin makaranta.