Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya ce talauci da rashin ilimi suna daga cikin manyan dalilan da ke sa Boko Haram ke dawowa a yankin Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali, yayin wata ziyarar ban girma da ‘yan Executive Intelligence Management Course 18 daga Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NISS) suka kai masa.
- Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
- Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
Gwamna Buni ya ce sai an magance talauci da rashin ilimi kafin a samu zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya ce idan ba a magance waɗannan matsaloli ba, rikicin zai ci gaba.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana aiki tuƙuru wajen rage talauci da bunƙasa ilimi ta hanyar shirye-shiryen taimakon tattalin arziƙi, gyaran makarantu da ɗaukar sabbin malamai.
Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp