Wata gobarar iskar gas ta tashi a Sabon Wuse, ƙaramar hukumar Tafa a Jihar Neja, a ranar Lahadi, kusan wata guda bayan fashewar tankar mai a Dikko Junction, kan titin Abuja-Kaduna.
Sabon Wuse na tazarar kilomita uku daga Dikko Junction, inda haɗarin tankar mai ya faru a baya. Wannan fashewar ta faru ne yayin da ake sauke lodin gas.
- Sojoji Sun Kai Farmaki, Sun Kashe Ƴan Ta’adda Masu Yawa A Neja
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Sayar Wa ‘Yan Bindiga Da Boko Haram Babura A Neja Da Kaduna
Shugaban hukumar kula da afkuwar bala’o’i ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa:
“Wata tashar kamfanin gas mai suna Tasiu Gas, kusa da Kalasma Filling Station a Sabon Wuse, kan babban titin Kaduna, ya fashe kuma ya kama da wuta.”
Sai dai ya bayyana cewa babu asarar rai, amma gobarar ta lalata motocin da shaguna da ke kusa da wurin.
Cikakkun bayanai na tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp