Wata mota dauke da iskar gas a daren ranar Juma’a ta kama wuta a unguwar Gwagwa da ke babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya sa mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da manema labarai ya ce motar ta yi bindiga ne da misalin karfe 8:30 na dare, kusa da wani wuri da ‘yansand ke tsayawa.
- Dan Nijeriya Ya Kafa Tarihi A Gasar Siriya A Daga Afirka
- Real Madrid Na Zawarcin Harry Kane Domin Maye Gurbin Benzema
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce, “A ranar 9 ga watan Yuni 2023, da misalin karfe 9 na dare, wata tankar mai dauke da gas ta samu matsala a dai-dai makarantar firamare ta Gwagwa da ke hanyar Gwagwa-karmo.
“Ana haka ne tartsatsin wuta ya sanya motar yin bindiga, inda tankar ta kone kurmus, amma ba a samu asarar rai ba.
“A halin yanzu an fara gudanar da bincike don sanin abin da ya haddada konewar motar.”