Biyo bayan ƙaddamar da kamfanin sarrafa fata da uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu, ta ƙaddamar a Legas, don samar da ayyukan yi ga matasa fiye da dubu goma tare da kawo wa jihar kudin shiga na kusan dala miliyan 250 a duk shekara.
Wannan ci gaban ya jawo martani daga Salihu Tanko Yakasai, wanda ya yaba da hangen nesan da jihar Legas ta nuna, amma ya bayyana takaicinsa kan yadda jihohin da ke samar da fata a Arewa, musamman Kano da Sokoto, ba su da irin wannan katafaren kamfani.
- Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP
- NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru
A cewarsa, jihohin nan ne suka fi samar da fatar da ake amfani da ita a masana’antu na kasashen Turai irin su Italy da Spain, wadda ake kera takalma da jakunkuna masu tsada da alfarma, inda ya tunatar da cewa tun kafin zuwan Turawa, Kano ta shahara wajen fitar da fata zuwa Morocco, wadda ita kuma take siyarwa ga Turawa.
Ya nuna bacin ra game da cewa duk da kasancewar Kano na da masana’antar gyara fata (tannery), har yanzu ba ta da babbar cibiyar da ke sarrafa fatar zuwa kayayyakin alatu kamar yadda Legas ke ƙoƙarin yi yanzu.
Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu.
Ya bayyana roƙo ga gwamnatin Kano ta yanzu da ta mayar da hankali wajen tabbatar da isasshiyar wutar lantarki, musamman ta hanyar wutar solar ko haɗin gwuiwa da manyan kamfanoni kamar Dangote da BlackRhino, don farfado da masana’antun jihar.
A cewar Yakasai, damuwa mafi girma ita ce yadda albarkatun Arewa ake dauka zuwa wasu jihohin kudu don a sarrafa, daga bisani kuma a dawo da su a sayar wa ’yan Arewa, tsarin da ya ce ya na barin Arewa a matsayin mai samar da kayan albarkatu kawai, yayin da sauran yankuna ke samun ayyukan yi da kuɗaɗen shiga daga sarrafa su.
Wasu matasan Kano a shafukan sada zumunta sun bayyana damuwarsu kan bai wa wasu abubuwa muhimmanci fiye da samar da irin waɗannan kamfanoni da za su gina rayuwar matasa da daƙile ayyukan daba da ya addabi jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp