Tun bayan da kasar Amurka ta sake hawa kujerar na ki game da kudurin da aka gabatar a zauren kwamitin tsaron MDD, don gane da gaggauta tsagaita wuta a Gaza a kwanan baya, masharhanta ke ta sukar wannan mataki na Amurka, wanda ko shakka babu ya kara ingiza alummar Gaza cikin karin tashin hankali da yanayi na rashin tabbas.
Alal hakika, abun takaici ne ganin yadda mambobin kwamitin tsaron MDD har 14 suka nuna amincewa da wannan kuduri, amma Amurka ta yi fatali da wannan matsaya tasu, a wani yanayi mai ban takaici da haifar da koma baya, wanda zai wanzar da tashe-tashen hankula da ake gani a Gaza, sama da watanni 13 da sake barkewar rikicin yankin.
- Akpabio Ya Karɓi Baƙuncin Dattawan Niger Delta, Karanta Abin da Suka Tattauna
- Gwamna Yusuf Ya Mika Motocin Bas Na CNG Guda 10 Ga Kungiyar NLC Reshen Kano
Idan mun waiwayi baya, za mu ga cewa Amurka ta hau kujerar na ki game da wani kudurin makamancin wannan a ranar 18 ga watan Oktoban bara, lokacin da tuni adadin fararen hula da suka rasu sakamakon rikicin Gaza ya kai kusan mutum 3,000. A karo na biyu da Amurka ta dauki wannan mataki, adadin fararen hular da hare-haren Israila ya hallaka a Gaza ya kai mutum 17,000. Haka dai Amurka ta ci gaba da daukar wannan mataki na hawa kujerar na ki game da kudurin gaggauta kawo karshen wannan rikici, har zuwa karo na 5, inda a ranar 18 ga watan Afrilun bana ta kara hawa kujerar na ki, a gabar da tuni adadin alummun Gaza da suka rasu sanadin wannan rikici suka karu zuwa mutum 34,000.
A halin da ake ciki yanzu kuwa, wannan adadi ya kai kusan mutum 44,000, amma Amurka ba ta sauya matsaya ba. Hakika wannan lamari ne mai matukar bakanta ran duk wani mai hankali da kaunar zaman lafiya. Adadin mutum 44,000 ba dan kadan ba ne, ya kuma kunshi yara kanana, da mata masu renon jarirai, da masu daukar nauyin bukatun iyalai cikin magidanta, wadanda asarar ran ko wane daya daga cikinsu, ke haifar da tashin hankali da damuwa ta tsawon rayuwa ga zuriyarsa.
Don haka, na kan tambayi kai na, shin anya rayuwar Falasdinawa na da wata daraja a idanun gwamnatin Amurka kuwa? Ko Amurka na iya waiwayar wadannan alummu da idon rahama da tausayawa? Abun da na yi imani da shi, shi ne ko bayan kawo karshen wannan tashin hankali, tabbas tarihi zai ci gaba da tunawa da mummunar matsayar Amurka game da matakan nan da take dauka a yanzu, tare da yin tir da halin ko in kula da rayukan dubban Falasdinawa mazauna zirin Gaza. (Saminu Alhassan)