Shi kuma ɓangaren Yamma da yake Yarabawa sune waɗanda suka fi gaggarumin rinjaye, a majalisar ta Sarakuna Shugabanta shi ne Sir Adesoji Aderemi, Oni na Ife. Sai kuma Sir Ladapo Ademola, Alake na Abeokuta; Oba J. O. Akapo Ake II, sai Olofin na Ado; Oba Aladesanmi II, sai Ewi na Ado-Ekiti; Obi Obika A. Gbenoba, ga kuma Obi na Agbor; Oba D. M. O. Fibigbade II, mai sarautar Ebumawe na Ago Iwoye; Chief F. M. Ogunlewe, shi ne Oloja na Igbogbo; Chief F B. O. Kalanama VI, shi ne Pere Kalanama na Akugbene; Oba Adegina II, shi ne Deji na Akure; Oba Olaseinde II, shi ne Ahaba na Ajagba; Oba L. O. Adenikiju, shi ne Ajobu na Araromi.
Sai kuma majalisar Sakuna ta gabashin Nijeriya wadda ta ƙunshi sunayen Prince Eugene William Dappa Pepple, shi ne Amanyanabo na Bonny, Chief J. T. Princewill Amachree VI shi kuma shi ne Amanyanabo na Kalabari, Buguma; Chief Kanu Oji, tshi ne Eze Aro na Arochuku; Chief James Okosi II, shi ne Obi of Onitsha; Chief Ika Ika Oƙua II, shi ne Ntoe na Big Ƙua,Calabar,da sauransu.
- Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo
- Koyo Daga Tarihi Da Kiyaye Zaman Lafiya Za Su Sa Kaimi Ga Zamanantar Da Duk Duniya Baki Daya
Sassan Nijeriya uku a lokacin sun samu dama da kuma ƴan ci, sai dai kuma shi ɓangaren su Sarakunan gargajiya wani ɓangare ne na ita gwamnatin sashen. Suna bada muhimmiyar gudunmawa saboda kuma akan nemi shawararsu, a dukkan matakan da aka ɗauka na gyaran tsarin mulki, da duk wani ci gaban da aka samu, wani abu kuma na ban mamaki shi ne babu wani lokacin da aka taɓa kawo masu wata barazana dangane da matsayin da suke da shin a Sarautar gargajiya.
Ba abin da ya dace bane a haɗa su da wata majalisar gargjiya wadda take ƙarƙashin mulkin Turawa da ake kiranta da suna House of Lords.
Alal misali Sarki shi Shugaba ne a masarautarsa a Arewa, hakanan ma shi Chief, a wurin mutanen da yake jagoranta, kasancewar sa majalisar Sarakuna ba wani abu bane nay a burge ko kuma ya yi wa gargajiya laifi. Ana bada muhimmiyar gudunmawa wajen tafiyar da harkokin mulki a wurin da yake mulka da kuma majalisar sashen da yake musamman ma a wancan lokacin kpo zamanin mulkin mallaka da Turawan Ingila suka aiwatar da shi mulki.Ba tare da shi ba mulkin zai fuskanci wasu matsalolin da ba za suyi ma shi kyau ba.
Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin.
Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da tsaronsu, ta haka ne za su fara wasu tafiye- tafiye basu nan basu can, wanda idan ba sa’a aka yi ba, kusan ƙarshen ƙasar ke nan a matsayinta na tarayyar Nijeriya a lokacin. Duk wani ƙoƙarin da Abubbakar Tafawa Balewa ya yi na kasancewa ya zama kamar yadda Kwame Nkrumah na Ghana, wanda a zamaninsa kome ya ce daidai ne sai an bi ko amfani da shi, irin hakan ba zai iya haifar da ɗa mai ido ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp