Tawagar ‘yan wasa mata ta Nijeriya ita ce tawaga daga Afirka guda daya kacal da ta fafata a gasar cin kofin duniya ta mata a shekarar 1991 da kasar China ta karbi bakunci.
Sai dai Nijeriya wadda mai koyarwa Jo Bonfrere ya jagoranta ba ta tabuka abin arziki ba a gasar bayan da suka kammala wasannin suna cikin rukuni a matsayi na karshe bayan sun sha kashi a hannun kasashe Jamus da Italy da kuma China.
Har ila yau, tawagar ta Nijeriya ta shiga jerin sunayen kasashen Amurka da Brazil da Norway da Japan da Germany da kuma Sweden a mastayin kasashe 7 da suka fafata a gasar kofin duniya ta mata karo tara a jere a jere.
Gasar da Nijeriya ta fi yin kokari ita ce a shekarar 1999, a lokacin da suka kai wasan kusa da na kusa da na karshe sai dai kasar Brazil ta doke Nijeriya bayan samun nasara da ci 4-3.
Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Wakilci Nijeriya A Gasar ta 1999
Masu Tsaron Raga
Ann Chiejine Diana da Lydia Koyonda.
‘Yan Wasan Baya
Nwaiwu, Ngozi Ezeocha, Omo-Lobe Branch, Mabis Ogun, Phoebe Ebimiekumo, Edith Eyuma
‘Yan Wasan Tsakiya
Nkechi Mbilitam, Florence Omagbemi, Nkiru Okosieme, Ann Mukoro, Rachael Yamala
‘Yan Wasan Gaba
Adaku Okoroafor, Chioma Ajunwa, Rita Nwadike, Ngozi Uche, Gift Showemimo
A halin da ake ciki kuma, yayin da Nijeriya take ci gaba da fafatawa a gasar ta bana da kasashen Australia da New Zealand ke karbar bakunci, Nijeriya ta buga canjaras da kasar Canada a wasan farko kuma ta fafata wasa na biyu da daya daga cikin masu masaukin baki wato Australia a ranar Alhamis.
Nijeriya ta fito a cikin rukuni na B da ya hada da kasashen Canada da Australia da kuma Jamhuriyar Ireland.