An gudanar da taron tattaunawa na “1+10” a nan kasar Sin a kwanan baya, inda jami’an wasu muhimman kungiyoyin duniya masu alaka da tattalin arziki, ciki har da sabon bankin samun ci gaba wato NDB, da bankin duniya da IMF, da kungiyar WTO, da kuma kungiyar raya ciniki da samun bunkasuwa ta MDD wato UNCTAD, suka halarci taron, don tattaunawa, da cudanya da manyan jami’an gwamnatin kasar Sin.
Masanan Sin masu nazarin siyasa da tattalin arzikin duniya, sun nuna cewa, an gudanar da wannan taro a lokaci mafi dacewa. Kuma Sin na bukatar kara hadin gwiwa da kungiyoyin kasa da kasa, duba da cewa tana nacewa ga manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin mabambantan bangarori, da kiyaye tsarin yin ciniki cikin ’yanci, da dukunlewar duniya a bangaren tattalin arziki.
- Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Ghana
- Kotu Za Ta Saurari Ƙalubalantar Ikonta Da Emefiele Ke Yi Kan Shari’arsa
A wani bangare na daban, Sin tana kokarin zurfafa matakan da take dauka bisa tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofarta ga waje. Tana kuma habaka bude kofarta ga ketare bisa jeren matakai, abin da ya baiwa masu zuba jari, da ’yan kasuwar duniya kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar.
Wasu ’yan kasuwa na kasashen waje na ganin cewa, manufar da Sin take dauka ta habaka bukatunta a cikin gida, na ci gaba da ingiza kuzari da karfin kasuwanninta, da karfin sayayyarta, matakin da ya samar da damammaki ga kamfanoni masu jarin waje dake zuba jari a kasar ta Sin. (Amina Xu)