Babban darakta a sashen nazarin tattalin arzikin kasa da kasa, karkashin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Li Kexin, ya ce an cimma manyan nasarori a taron BRF da aka kammala a nan birnin Beijing.
Li, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce yayin dandalin da ya samu halartar manyan shugabannin duniya da dama, an cimma nasarorin da suka kai 458, wanda hakan ke nuna kyakkyawan fata da ake da shi, na hada karfi da karfe wajen bunkasa shawarar ziri daya da hanya daya, zuwa wani sabon matsayin ci gaba mai inganci.
- Xi Ya Aika Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 110 Da Kafuwar Kungiyar Daliban Sin Dake Turai Da Amurka
- Yadda Yaki Da Hamada Ke Samar Da Kudin Shiga A Jihar Xinjiang
Li Kexin ya kara da cewa, Sin za ta aiwatar da wasu manyan tsare tsare 8, don gina shawarar ziri daya da hanya daya mai inganci, wanda hakan ke nuna aniyar kasar ta nacewa, da imanin ta ga manufar bunkasa duniya da samar da wadata, da ma zamanantar da dukkanin kasashen duniya.
Daga nan sai jami’in ya ce dubban wakilai daga sama da kasashen duniya 150, da hukumomin kasa da kasa sama da 40, ciki har da shugabannin kasashen waje 23, da babban magatakardar MDD, sun halarci taron. Kuma dukkanin su sun amince da cewa taron na BRF, wani muhimmin dandali ne na ingiza gina shawarar ziri daya da hanya daya tare.
Ya ce taron ya fitar da sanarwar shugaba, game da manyan sakamakon da aka cimma, mai kunshe da jerin takardun bayanai da jerin ayyuka, wadanda adadin su ya kai 458. Kaza lika, Sin da wasu kamfanonin ketare, sun cimma matsayar gudanar da ayyukan hadin gwiwa da darajar su ta kai dala biliyan 97.2.
Wadannan nasarori sun zamo tamkar kuri’u na goyon baya, da nuna amincewar akasarin abokan huldar shawarar ta ziri daya da hanya daya. (Saminu Alhassan)