Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta ce, ta yi dukkan shirye-shirye domin karbar bakuncin taron kungiyar BRICS ta kasashe masu samun saurin ci gaban tattalin arziki karo na 15, da zai gudana daga ranar 22 zuwa 24 ga wannan wata.
A karon farko tun bayan barkewar annobar COVID-19, shugabannin kasashen Brazil da Rasha da India da Sin da kuma Afrika ta Kudu da suka hada kungiyar BRICS, za su yi taro ido da ido, wanda ake ganin zai kasance wata zaburarwa ga kasashe masu tasowa musamman ma nahiyar Afrika da a bana za su karbi bakuncin muhimmin taron.
Bisa la’akari da ka’idojin kungiyar BRICS na aiwatar da hadin gwiwa bisa girmama juna da kaucewa tsoma baki da kuma tabbatar da daidaito, BRICS ta gabatar da wani sabon salon hadin gwiwa a duniya, haka kuma ta kasance wata dama da kuma fata ga kasashe masu tasowa da aka dade ana ci da guminsu.
Taken taron na bana “BRICS da Afrika: Hadin gwiwa domin gaggauta samun ci gaba tare, ci gaba mai dorewa da huldar kasa da kasa da dukkan bangarori” na nuni da cewa, BRICS na da burin tafiya da nahiyar Afrika da kuma samar da damarmaki. Idan muka yi duba da kasashen kungiyar, mun san cewa kasashe ne dake samun saurin ci gaba ta hanyar dogaro da kansu da al’ummarsu, haka kuma kasashe ne masu kaunar a gudu tare a tsira tare, musamman kasar Sin dake kokarin ganin an gina duniya mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.
Yadda kasashe da dama kusan sama da 40 suka bayyana sha’awar shiga kungiyar, ya nuna cewa tana da ma’ana, kuma dama ce da nahiyar Afrika ke bukata musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsaiko a fannonin mu’amalar kasa da kasa. Wannan kungiya za ta ba nahiyar Afrika damar koyon dabarun ciyar da kanta gaba, da hadin gwiwa ta moriyar juna bisa adalci da kuma samun moriyar juna. Nahiyar Afrika na bukatar hadin gwiwa da kasashe irin Sin da Rasha da suka tsaya kai da fata wajen yaki da danniya da babakere. Yadda Afrika ta kudu mai masaukin baki ta gayyaci shugabannin kasashen Afrika zuwa taron, ya bude wata kafa da kasashen za su gabatar da irin albarkatun da suke da shi da bangarorin dake bukatar gogewa da kwarewar wadannan kasashe domin su ci gajiyar abubuwan da suka mallaka ta hanyoyin da suka dace ba na ci da gumi ba. Haka kuma, kasancewar wadannan kasashe masu yanayi da al’umma kamar kasashen Afrika, dama ce ta koyon dabarunsu domin shawo kan kalubalen da suke fuskanta.
La’akari da kasar Sin a matsayin mai ruwa da tsaki a kungiyar BRICS, a ganina, kasashen Afrika ba su da wata matsala da wannan kungiya, domin har kullum kasar Sin kan wuce gaba wajen kare moriyarsu da tallafa musu. Kuma na yi imanin kungiyar BRICS wata kafa ce da za ta hada kan kasashe masu tasowa wajen kai su ga samun ci gaba mai dorewa. Haka kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da a nan gaba, an samu kasashe da dama a duniya masu karfi da wadata, ba wai wasu ’yan tsiraru kadai su yi babakere ba.