Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, yayin da a nahiyar Afirka ce aka fi samun kasashe masu tasowa, inda yawan al’ummun bangarorin 2 a baki daya ya kai kashi 1 cikin kashi 3 na daukacin al’ummun duniya. Wannan shi ne dalilin da ya sa taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing na Sin a kwanan baya zama wani kasaitaccen biki na “Global South” wato daukacin kasashe masu tasowa, inda dimbin nasarorin da aka cimma suka nuna kwarin gwiwar kasashe masu tasowa na gudanar da hadin kai tsakaninsu.
A wajen taron, an kara kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka: Kasar Sin ta kulla huldar abota ta manyan tsare-tsare ko daukaka huldar tare da karin kasashe 30 dake nahiyar Afirka, ciki har da Najeriya. Haka zalika, an daga matsayin huldar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa na al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya na sabon zamani a duk wani yanayin da ake ciki.
- Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Al’ummar Borno Kan Ambaliyar Ruwa
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Budewar Dandalin Mata Na SCO
A fannin neman ci gaba na bai daya, shugabannin kasashen Afirka sun yarda da shawarar da kasar Sin ta gabatar dangane da “wane nau’in zamanantarwa ya kamata a nema”, wadda ta zama matsaya daya da bangarorin Sin da Afirka suka cimma ta fuskar harkokin siyasa. Ban da haka, bangarorin 2 sun tabbatar da shirinsu na hadin gwiwa na shekaru 3 masu zuwa, da tabbatar da cikakken tsarin aikin zamanantar da kasa.
Kana a fannin samar da adalci a duniya, bangarorin Sin da Afirka sun amince da rufawa junansu baya, musamman ma ta fuskar manyan batutuwan da suka shafi babbar moriyarsu, don kare hakkin kasashe masu tasowa. Ban da haka sun yarda da aiwatar da manufar kasancewar dimbin bangarori masu fada a ji, da kin ra’ayin nuna bambanci, da sanya aikin zamanantarwa amfanar daukacin jama’a.
Sa’an nan ya kamata a lura da cewa, a wajen taron, kasar Sin ta jaddada niyyarta ta musayar fasahohin gudanar da mulki tare da kasashen Afirka, da nuna wa kasashe daban daban goyon baya kan yadda za su zabi hanyar zamanantarwa mai dacewa da yanayin da suke ciki, da tabbatar da daidaituwa tsakanin mabambantan kasashe ta fuskar hakki da damammaki. Yayin da a fannin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka da sauran kasashe suke yi, kasar Sin ta ba da shawarar tabbatar da adalci, da daidaito, gami da samar da hakikanin sakamako. Ta haka za a iya fahimtar matsayin kasar Sin na kare hakkin kasashe masu tasowa, da tabbatar da adalci a duniya.
Sai dai, ko da yake taron na wannan karo ya nuna yadda Sin da Afirka suke kokarin hadin gwiwa da juna, da neman ci gaba tare, da kare adalci a duniya, amma kafofin yada labaru na kasashen yamma na ci gaba da korafe-korafe kan taron FOCAC da huldar dake tsakanin Sin da Afirka. Masu sharhi na kasashen yamma su kan kalli cudayar da Sin da Afirka suke yi a matsayin wani aikin da aka yi, musamman ma domin takara da kasashen yamma, ta fuskar neman albarkatun kasa, da samar da tasiri a duniya. Amma wannan ra’ayi nasu bai tabo tushen huldar dake tsakanin Sin da Afirka ba.
Idan mun yi bitar takardun yarjejeniyoyin da bangarorin Sin da Afirka suka cimma, da sakamakon da aka samu a hadin gwiwarsu, za mu ga cewa raayin girmama juna shi ne tushen huldarsu, da gudanar da hadin gwiwa ta wata sahihiyar hanya, da neman ci gaba tare da amfanin juna. Wannan hulda ta zarce musayar moriya, da tsarin ba da tallafi da kasashen yamma suka saba yi na nuna girman kai, ta kuma dace da akidar hadin kan kasashe masu tasowa ta amfanin juna, da girmama ikon mulkin kai, da kokarin cimma burin samun bunkasuwar bai daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa shugaba Bola Tinubu na kasar Najeriya ya bayyana a wajen taron kolin FOCAC na wannan karo cewa, “ Nasarar da aka cimma a FOCAC ta nuna cewa, ba lallai ba ne a ci nasara daga faduwar wani bangare a yayin da kasa da kasa ke neman tabbatar da ci gabansu” A cewarsa, ta hanyar kokarin neman tabbatar da moriyar juna, bangarorin Sin da Afirka sun samar da dimbin damammakin raya al’umma da samun walwala.
“Huldar dake tsakanin Afirka da Sin ta zama abin koyi a fannin hadin gwiwar kasashe masu tasowa”, wannan jimla tana cikin maganar da shugabannin kasashen Afirka suke maimaitawa a taron FOCAC na wannan karo. A nasa bangare, Antonio Guterres, babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, wanda shi ma ya halarci taron, ya ce, “Huldar dake tsakanin Sin da Afirka gishiki ne ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa. ”Hakan ya nuna cewa, wadannan manyan kusoshin duniya sun fahimci tushen huldar dake tsakanin Sin da Afirka. Kana tabbas wannan tushe zai sa hadin gwiwar Sin da Afirka ci gaba da samar da gudunmowa ga karuwar karfin daukacin kasashe masu tasowa a duniya. (Bello Wang)