A kwanakin baya ne, kungiyar kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato G7 a takaice, ta gudanar da taronta a birnin Hiroshima na kasar Japan.
Sai dai sabanin abin da ya kamata kungiyar ta tattauna game da abubuwa dake addabar duniya a halin da ake ciki, tare da zakulo hanyoyin magance su, sai ta kauce hanya tana shiga sharo ba shanu, ta hanyar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, musamman kasar Sin.
Wannan ya sa bangaren kasar Sin ya nuna adawa da yadda kungiyar ta G7 take tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da neman bata mata suna, da ma cutar da muradun kasar ta Sin.
Yayin taron na wannan karo, shugabar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai wato EU, Ursula von der Leyen, ta yi wasu kalamai marasa dacewa kan kasar Sin, wannan ya sa bangaren Sin, ya kalubalanci kasashen na G7 cewa, Idan har da gaske kasashen G7 suna maida hankali kan kasashe masu tasowa, to, ya dace su cika alkawarin su ba tare da bata lokaci ba, wato amfani da kaso 0.7 bisa dari na daukacin kudin shigar su a kowace shekara don tallafawa kasashen, da samar wa kasashe masu tasowa jarin dala biliyan 100 a fannin sauyin yanayi a kowace shekara, tare kuma da kara daukar nauyin kasa da kasa, da kara yin abubuwan kirki na zahiri a kasashe masu tasowa. Mu gani a kasa, Wai an ce da kare ana biki a gidansu.
A sanarwar Hiroshima da shugabannin kasashen G7 suka fitar kan kwance damarar makaman nukiliya ma, sun soki manufofin gwamnatin kasar Sin kan makaman nukiliya. Sanin kowa ne cewa, wannan ba shi ne ainihin abin da ya kamata kasashen kungiyar su tattauna ba, dadin dadawa ba kungiyar G7 ce take da ikon tsara ka’idojin hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa ba, ma’ana ba ta da hurumin baiwa sauran kasashe umarni a wannan fanni.
A don haka, kamata ya yi kungiyar ta tsaya cikin huruminta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar da ma ci gaban duniya baki daya, maimakon zama ‘yar kanzakin wasu kasashe don neman kare muradunsu.
Wannan ya nuna a fili yadda kungiyar G7 baki daya, ta bar Jaki tana dukan Teki, inda ta kauce daga muhimman abubuwan da ya kamata ta tattauna a wannan lokaci da duniya ke fama da manyan kalubaloli da ya dace a kai ga samo bakin zaren warwaresu. Masu iya magana na cewa, kowa ya debo da zafi bakinsa.