Taron ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya jaddada bukatar kara hadin kai, don aiwatar da manyan shawarwari da tsare-tsare da aka cimma a yayin babban taron wakilan JKS karo na 20.
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya gabatar da muhimmin jawabi a lokacin da yake jagorantar taron suka da suka da kai da aka gudanar daga ranar Litinin zuwa jiya Talata.
An jaddada a yayin taron cewa, bana shekara ce mai matukar muhimmanci a tarihin jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya.
A cewar taron, a yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye, kana akwai ayyuka masu wahala da kalubale a fannin gyare-gyare da raya kasa da tabbatar da zaman lafiya a cikin gida, kwamitin kolin JKS bisa jagorancin Xi Jinping ya hada kai tare da jagorantar jam’iyyar da ma al’ummar Sinawa, don tunkarar kalubalen da za su iya kunno kai, da tabbatar da daidaiton tattalin arziki da zamantakewa baki daya.
Taron ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar ya ci gaba da samun bunkasuwa mai kyau a cikin shekarar, tare da cikakken kwanciyar hankali a cikin ayyukan yi, daidaiton farashi da kuma harkokin cinikin duniya.
Haka kuma taron ya bayyana cewa, yawan hatsin da kasar Sin ta samu ya zarce tan miliyan 650 a cikin shekaru takwas a jere, tare da tabbatar da isasshen abinci, da makamashi da kuma jin dadin jama’a yadda ya kamata.
Taron ya kara da cewa, kasar ta yi nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da na nakasassu na shekarar 2022 da aka gudanar a birnin Beijing, duk wadannan nasarorin da aka cimma, ba a same su cikin sauki ba, don haka, ya kamata a girmama su sosai.(Ibrahim)