An gudanar da taron kara wa juna sani kan bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da fitar da su kasar Sin karo na 137, wanda ake kira da ‘Canton Fair’, da ake gudanarwa duk shekara a birnin Guangzhou na kasar Sin, tun daga shekarar 1957, jiya ranar Alhamis a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Taron karawa juna sanin ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin kasar Habasha, da wakilai daga kungiyoyin ‘yan kasuwa na Habasha da Sin, da tawagar kasar Sin da jami’an diflomasiyyar Sin dake kasar Habasha.
- NAHCON Ta Naɗa Sabon Sakatare
- Shirin Zamanantar Da Aikin Noma Na Sin Na Samar Da Damar Bunkasa Bangaren A Afirka
Mahalarta taron sun ce bikin baje kolin na Canton Fair na taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu da ma sauran kasashen duniya.
Da yake jawabi a taron, babban sakataren kungiyar ‘yan kasuwa da kungiyoyin sassan harkoki na kasar Habasha (ECCSA), Kenenisa Lemi, ya ce bikin Canton Fair wani ginshiki ne na ci gaban kasuwanci na duniya da aka dade da samu.
Ya sake nanata kudiri da kara himmar kungiyarsu ta ECCSA wajen saukaka hanyoyin halartar bikin baje kolin da ke tafe ga masu masana’antun Habasha da masu shigo da kayayyaki daga kasashen waje na kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp