Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya.
Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya.
Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga jama’arsu da yawanta ya kai biliyan biyu, kana ya samar da babbar gudummawa ga raya zaman lafiya, da ci gaban duniya baki daya. Kazalika, hadin gwiwar sassan biyu ya zamo misali na hadin gwiwar cimma moriyar juna, a sabon zamani na dunkulewar tattalin arzikin duniya.
Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da EU, wajen cimma nasarar taron, matakin da zai aike da kyakkyawan sako ga duniya, game da aniyarsu ta hada karfi da karfe, wajen kafa hadin gwiwa mai karfin gaske, da daga martabar cudanyar mabambantan sassa, da bude kofa da aiwatar da hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)














