Taron kolin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar nahiyar Asiya wanda ya gudana a birnin Xi’an na lardin Shaanxi, ya jawo hankalin kasa da kasa matuka.
A zantawarsa da wakilin babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ministan masana’antun kasar Pakistan, Tasneem Ahmed Qureshi ya ce, taron kolin, babban abun misali ne dake shaida kokarin kasar Sin, na samar da ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da inganta mu’amalar wayin-kai a wannan shiyya. Ya ce, a matsayinta na kasa mai tasowa, Sin ta fahimci cewa ya dace a samar da zarafin neman ci gaba mai adalci ga wadannan kasashe. Sabili da haka, kasar Sin tana kokarin samar wa sauran kasashe masu tasowa damammakin neman ci gaba.
Tasneem na ganin cewa, ba maida hankali kan samar da ci gaban kanta kawai kasar Sin take yi ba, har ma tana nuna kwazo wajen samar da ci gaba ga dukkan shiyyar.
Ya kuma soki lamirin wasu kasashe, wadanda ke amfani da tada zaune-tsaye ko rura wutar rikici tsakanin kasa da kasa don biyan bukatun muradun kansu, inda a cewar sa, shawara gami da matakin kasar Sin na da ma’ana sosai, wanda ya bambanta da manufofin da ka iya haifar da barna. (Murtala Zhang)