Ministan babban birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Bello, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin shekaru bakwai da rabi da suka gabata ta sake sauya fasali da farfado da tattalin arzikin Nijeriya tare da dora shi kan turba mai dorewa fiye da dogaro a bangaren man fetur da iskar gas kacal.
Ministan, wanda ya bayyana hakan a wajen taron shekara-shekara na LEADERSHIP da bayar da kyautuka na shekarar 2022 da aka yi a Abuja ranar Talata, ya ce gwamnatin ta mai da hankali sosai kan bangaren harkar noma da ma’adinai da kuma cigaban kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs).
Taron mai taken ‘Sahihancin Zabe da sauyin Tattalin Arziki’, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Tsohon Fira Ministan Kenya, Raila Odinga ne suka jagoranci taron.
Ministan ya kara da cewa, matakin da gwamnati ta dauka ya sanya tattalin arzikin Nijeriya kan turba mai dorewa wacce za ta cigaba da farfado da tattalin arzikin kasar, ta hanyar Sahihancin zabe ne aka samu wannan nasara inda gwamnati mai jiran gado za ta dora kan inda shugaba Buhari ya tsaya.