Taron masana’antu da kasuwanci na kasashen BRICS dake tafe, ya bayyana yadda ‘yan kasuwa a duniya ke da kwarin gwiwa kan makomar ci gaban tattalin arzikin Sin, da kuma sha’awarsu ta karfafa hadin gwiwa da ita.
Zhang Shaogang, mataimakin shugaban kwamitin inganta cinikayya da kasashen ketare ta kasar Sin CCPIT ne ya bayyana hakan ga wani taron manema labarai a jiya, inda ya ce, baya ga kasashen BRICS, taron ya ja hankalin mahalarta daga kasashe 13 ciki har da Kazakhstan da Argentina da Thailand da kuma Indonesia.
A cewarsa, galibin kamfanoni da za su halarci taron, sanannu ne a duniya kuma muhimmai a kasashen BRICS, ciki har kamfanoni 40 na jerin manyan kamfanoni 500 na duniya, da suka shafi bangarorin makamashi da hada-hadar kudi da kere-kere da kuma na zamani masu tasowa, kamar na intanet da manyan bayanai da cinikayya ta intanet da sabon makamashi.
A cewar Zhang Shaogang a taron, kawancen kasashen BRICS da suka hada da Brazil da Rasha da India da Sin da Afrika ta Kudu, da su ne suka mamaye kaso 23 na tattalin arzikin duniya da kaso 18 na cinikayyar kayayyaki da kaso 25 na jari a kasashen waje, wani muhimmin karfi ne da ba za a iya watsi da shi wajen ingiza tattalin arzikin duniya ba. (Fa’iza Mustapha)