Alkaluman da tashar jiragen ruwa ta Shanghai ta fitar jiya Litinin na nuna cewa, duk da barkewar annobar COVID-19, tashar ta kasance mafi hada-hadar kwantenoni a duniya a cikin shekaru 13 a jere a shekarar 2022.
A cewar rukunin kamfanin kasa da kasa dake kula da tashar, wato Shanghai International Port (Group) Co., Ltd a Turance, adadin kwantenonin da aka yi jigilarsu ta tashar jiragen ruwan a shekarar 2022, ya zarce miliyan 47.3 (TEUs). (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp