ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: INEC Za Ta Dauki Ma’aikata Miliyan 1.4 Domin Horar Da Su Fasahar BVAS – Okoye

by Sulaiman
4 years ago
INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce ta fara shirye-shiryen ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi domin fara horas da su yadda za su yi aiki da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS.

Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da akayi da shi ƙarshen makon jiya, a gidan talbijin na Channels TV.

ADVERTISEMENT
  • Babu Wata Kafa Na Yin Magudin Zabe A 2023 – INEC

Ya ce akwai buƙatar bayar da horon ƙwarewa wajen yin amfani da BVAS ɗin, ta yadda a lokacin zaɓuka ba za a riƙa samun jinkiri ba, wanda hakan ka iya sa masu jefa ƙuri’a yin ƙorafi da tsarin tantance su ta hanyar amfani da BVAS ɗin.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Okoye ya ce za a wadatar da BVAS a dukkan rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin ƙasar nan.

Wani bincike kuma, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar har yanzu akwai aƙalla mutum milyan 1.7 da ba su karɓi katin shaidar rajistar zaɓe ba, wato PVC, a Jihar Legas.

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa ranar Asabar, mutum 5,816,528 ne su ka karɓi shaidar rajistar zaɓe a Jihar Legas.

Tuni dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara kokawa da yadda karɓar katin shaidar rajistar zaɓe ke tafiyar-hawainiya a wasu jihohin, ganin yadda jama’a ba su bayar da himma sosai wajen tururuwar zuwa a karɓi katin, wanda sai da shi ne mutum zai iya jefa ƙuri’a a zaɓukan Nijeriya.

Hakan ya sa cikin makon jiya INEC ta je Jihar Cross River, inda ta riƙa wayar wa jama’a kai cewa su hanzarta su je su karɓi katin shaidar rajistar zaɓen su.

Hukumar ta yi wannan kiran ne a wurin gagarimin taron kalankuwar ‘Calabar Carnival’.

A Jihar Akwa Ibom ma hukumar ta koka ganin yadda jama’a ba su yin tururuwar zuwa karɓar katin shaidar rajistar zaɓe.

A Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT) kuwa, rahotanni sun nuna cewa har yanzu akwai katin shaidar rajistar zaɓen da ba a karɓa ba, tun daga 2011 zuwa 2022, har guda 460,643.

Rahotannin sun nuna cewa daga 2011 zuwa 2019 akwai katin da har yanzu ba a karɓa ba, guda 230,007.

Sai kuma waɗanda aka yi wa rajista amma ba su karɓa ba daga 2021 zuwa 2022 har guda 230,636.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye, ya jaddada cewa INEC za ta yi amfani da na’urar tantance mai rajistar katin zaɓe, wato BVAS a dukkan rumfunan zaɓen ƙasar nan guda 176,846.

Sannan ya ce tuni INEC ta fara aikin yadda za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi fiye da milyan 1.4 waɗanda za a bai wa horon aiki da na’urar BVAS a lokacin zaɓukan shugaban ƙasa, na ‘yan majalisar tarayya, gwamnoni da na majalisar dokoki ta jihohi.

INEC
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Albarkacin Hutun Sabuwar Shekara An Gudanar Da Yawon Bude Ido Miliyan 52.7 A Kasar Sin

Albarkacin Hutun Sabuwar Shekara An Gudanar Da Yawon Bude Ido Miliyan 52.7 A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.