Farfesa Edward Dintwe, na sashen koyar da ilimin injiniya da fasaha, dake jami’ar Botswana, ya ce sannu a hankali, kasar Botswana za ta zama mai cikakken ikon fitar da wutar lantarki, domin sayarwa ga kasashe makwaftan ta, bayan da kamfanin CNEEC na kasar Sin, ta kammala ginin sashen B na tashar lantaki mai amfani da kwal ta Morupule.
Farfesa Dintwe, ya ce kammala tashar lantarkin, ya sauya matsayin kasar daga mai shigo da lantarki zuwa mai fitar da shi.
Rahotanni daga kamfanin samar da makamashi na kasar BPC na cewa, cikin watanni uku da suka gabata, sassan A da B, na tashar wutar lantarki ta Morupule, na aiki yadda ya kamata, inda suke samar da lantarki da ya haura MW 800 duk sa’a, adadin da ya haura bukatar makamashi ta kasar.
Shi ma yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan ma’aikatar makamashi da albarkatun kasar Lefoko Moagi, ya ce Botswana ta cimma nasarar fara sayar da lantarkinta ne, bayan da aka kammala sashen B na cibiyar lantarki ta Morupule, mai samar da MW 600 duk sa’a. Don haka kasar ke iya sayar da rarar lantarkin ta ga kasashe makwaftan ta.
Ya ce kasancewar Botswana kasa maras iyaka da teku, hanya daya tilo ta samar da makamashi ita ce ta amfani da kwal, kuma kafin shekarar 2010, tashar Morupule A ce kadai ake samu a kasar.
Daga bisani, kamfanin CNEEC na kasar Sin, ya gina sashen B na tashar, mai samar da karin MW 600 na lantarki ga kasar. (Saminu Alhassan)