ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashar Lekki Ta Sa Kaimin Bunkasuwar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka

by CGTN Hausa
2 years ago
Lekki

Yau ina tare da wani albishirin da zan so in gutsura muku. Tashar jiragen ruwa ta Lekki da ke birnin Lagos, ta riga ta samar da guraben aiki sama da 3,000 ga al’ummar wurin tun bayan da ta fara aiki a hukunce a watan Afrilun wannan shekara.

An ce, tashar Lekki na iya samar da guraben aiki kimanin dubu 170, kuma sama da kaso 90% daga cikinsu an samar da su ne ga mazauna wurin.

  • Manoman Kenya Na Kara Rungumar Fasahohin Inganta Noma Na Sin
  • An Yabawa Ci Gaban Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin Yayin Liyafar Da Aka Shirya Domin Murnar Cikarta Shekaru 74 Da Kafuwa 

Har wa yau, kasancewarta tasha mai zurfin ruwa ta zamani irinta ta farko a Nijeriya, wadda kuma ke daya daga cikin tashoshi masu zurfin ruwa mafiya girma a yammacin Afirka, yadda aka fara aiki da tashar Lekki, ya daidaita matsalolin koma bayan ababen tashar Lagos da ke yi wa ci gaban cinikin da Nijeriya ke yi da kasa da kasa tarnaki, wadda ta yi matukar kyautata kwarewar birnin Lagos ta fannin shige da ficen hajjoji.

ADVERTISEMENT

Ban da haka kuma, sakamakon yadda Nijeriya ta kasance kofar wasu kasashen da ke cikin Afirka, irinsu Chadi, da Nijer ta hadewa da teku, tashar ta Lekki, za ta kuma kara samar da karfin bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar.

Hadewa da juna ta bangaren manyan ababen more rayuwa, na daya daga cikin manyan burikan da ake neman cimmawa wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, a wani kokari na sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin shiyya, da ma na duniya baki daya. Kasancewarsa daya daga cikin nasarorin da aka cimma a gun taron kolin kasa da kasa karo na biyu kan shawarar ziri daya da hanya daya, tashar Lekki ba kawai ta taimaka ga ci gaban tattalin arzikin cikin gidan Nijeriya ba ne, har ma za ta zama muhimmiyar mahada ta teku, wanda hakan ya aza ingantaccen harsashi ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka baki daya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

November 17, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Daga Birnin Sin

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Next Post
2034: Nijeriya Na Goyon Bayan Saudiyya Ta Dauki Nauyin Kofin Duniya

2034: Nijeriya Na Goyon Bayan Saudiyya Ta Dauki Nauyin Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

November 17, 2025
Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

November 17, 2025
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

November 17, 2025
Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

November 17, 2025
Tsohuwar Firaministan Bangaladesh Sheikha Hasina,

An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa

November 17, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi

November 17, 2025
Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka

November 17, 2025
Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda

November 17, 2025
Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon

Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon

November 17, 2025
Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.