Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta ce tashin farashin kayan masarufi a Nijeriya ya kai kashi 31.70 cikin É—ari a watan Fabrairu.
Wannan na nuni da kari daga alkaluman baya na kashi 29.90 idan aka kwatanta da bara, daidai watan Fabrairu inda aka samu karin kashi 9.79.
- Mabambantan Wayewar Kai Ya Kara Kyautata Duniyarmu
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Kar A Fake Da Batun Dimokuradiyya Don Neman Biyan Bukatar Kai
Alkaluman NBS sun nuna yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya ya fi tsadar abinci, inda a Arewa maso Yamma aka fi samun rangwame
Mai taimaka wa shugaba Tinubu kan labarai,Abdul’aziz Abdul’aziz, ya ce don magance kunci ne ya sa shugaban ganawa da shugabannin kasashe masu arziki don zuba jari a Nijeriya.
Tun bayan cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi a ranar 29 ga Mayun 2023 aka shiga tsadar rayuwa a Nijeriya.
Tsadar rayuwar dai ta haifar da zanga-zanga a wasu sassan Nigeria, sai dai Tinubu ya yi burus da koken da mutane suka yi, inda ya ce ba gudu ba ja da baya game da batun cire tallafin man fetur.