An samu mummunan iftila’i a garin Pulka na ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, inda fashewar Gurneti ya kashe yara uku a yammacin jiya Alhamis. Yaran da suka mutu sun haɗa da Fati Dahiru, Aisha Ibrahim da Fati Yakubu.
Rahoton wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa, wani ɗan ƙungiyar CJTF, Buba Yaga, ya ce yaran na wasa da wani bam da ake zargin Boko Haram sun bari, kafin ya fashe da misalin ƙarfe 2:20 na rana.
- Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare
- Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno
Bayan faruwar lamarin, jami’an kunce bam (EOD) na Ƴansanda, da Sojojin Operation Haɗin Kai, da CJTF, da mafarauta sun isa wurin, suka kakkaɓe wajen, kuma ba su sake samun wani abu mai haɗari ba. An garzaya da yaran asibitin gwamnati na Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
An miƙa gawarwakin ga iyalansu don yin jana’iza bisa tsarin Musulunci, yayin da hukumomi suka shawarci jama’a su riƙa sanar da jami’an tsaro idan sun ga abubuwa masu haɗari domin kauce wa irin wannan bala’i.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp