Wata mummunar gobara da ta tashi a safiyar Litinin ta hallaka ‘yar Sakataren Gwamnatin Jihar Sokoto, Alhaji Muhammadu Bello Sifawa, tare da ‘ya’yanta uku. Marigayiyar ita ce matar Babban Sakataren Ma’aikatar Wasanni da Matasa ta Jihar Sokoto, Alhaji Muhammadu Yusuf Bello.
Gobarar, wacce ba a san musabbabinta ba, ta lakume gidan gaba ɗaya yayin da iyalin ke barci. Mijin marigayiyar shi kaɗai ne ya tsira, yayin da ma’aikatan kwana-kwana suka yi awanni suna fafutikar kashe gobarar.
- Gobara Ta Ƙone Kayayyakin Biliyoyin Naira A Rumbun Ajiya Na NSIPA Da Ke Abuja
- Gwamnatin Kano Ta Raba Naira Miliyan 12.7 Ga Mutane 281 Da Gobara Ta Shafa
Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Injiniya Idris Mohammed Gobir, tare da mambobin majalisar zartarwa, da jiga-jigan jam’iyyar APC, da abokai, da ‘yan uwa sun yi tattaki zuwa gidan Sifawa don yi wa iyalan ta’aziyya.