Yayin da ake bukukuwan cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong, karkashin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, tashoshin talabijin da radio na The Greater Bay masu gabatar da shirye-shiryen Documentary, na kafar yada labarai ta CGTN na kasar Sin, sun fara watsa shirye-shiryensu a yankin.
Tashar radio ta The Greater Bay, ta watsa bukukuwan murnar kai tsaye cikin harshen Cantonese na yankin daga cibiyar taruka da nune-nune ta HK. Daga cikin shirye shiryen da ta watsa, har da na kaddamar da sabuwar gwamnatin yankin.
Shirye-shirye da dama masu kayatarwa da aka gabatar kan maudu’ai daban-daban da aka watsa a ranar farko, sun ja hankalin mazauna yankin, inda kuma bangarori daban-daban daga Hong Kong din da Macao, suka yi ta aikewa da sakon taya tashar murna. (Fa’iza Msutapha)