Garba Muhammad, fitaccen jarumi ne da ke haskawa cikin shirin Labarina, wanda ya shafe tsahon shekaru 25 a wasan kwaikwayo na ‘Dabe’, kana ya shafe wasu shekaru masu yawa a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wanda tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa a yanzu.
Wanda aka fi sani da Abubakar Waziri, Garba ya bayyana wa masu karatu dalilansa na shiga harkar fim, yayin da gefe guda kuma ya bayyana irin salon da ya ke bi dan ganin ya kara bunkasa wasan nasa, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta fim. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi
Sunana Garba Muhammad amma an fi kira na da Abubakar Waziri
Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Ni haifaffen Samarun Zariya ne a Jihar Kaduna a takaice ni bazazzage ne, kuma na yi karatun firamare a Hayin Dogo Samarun Zariya, daga nan na tafi ‘Gobernment Day Secondary School’ dake Hayin dogo wadda yanzu ita ce ‘Gobernment Girls Secondary School Samaru’. Daga bisani na ci gaba da karatu a ‘ABU Zaria’ a Tsangayar Nazarin Al’adun Gida Nigeria (Center For Nigerian Cultural Study) ABU Zariya.
Wanne irin rawa kake takawa a masana’antar Kannywood?
Rawar da nake takawa dai ni Jarumi ne kuma na kan fita a kowane irin yanayin labari ya zo a kaina wanda ba zai taba mutuncina ko na iyalina ba ko addinina da al’ada ta ba.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin harkar fina-finai?
Abin da ya ja hankalina shi ne ina ganin wanna ita ce hanyar da zan mika sako da nake burin ya isa ga jama’a.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ya kasance ganin yadda wasu ke kuka da shigar kafin su samu a karbe su?
To da farko dai ni ban sha wahala sosai ba, saboda dama ina yin wasan kwaikwayo na dabe, sai aka yi dace wasu daga cikin masu shirya fina-finan suna kallon wasana wannan dalilin ya sa suka gayyace ni cikin harkar fim, kuma cikin hukuncin Allah, sai na ba da abin da ake so wannan shi ne sila.
To batun iyaye fa, lokacin da ka fara sanar musu kana sha’awar shiga cikin harkar, shin ka fuskanci wani kalubale daga gare su?
A bangaren iyayena ban samu wata matsala ba, saboda lokacin ina firamare ni mutum ne mai son wasa da dalibai, wani lokakacin na kan yi kwaikwayon malaminmu na harshen Hausa ina koya wa dalibai karatu ta irin sigar da yake amfani da ita, wannan shi ya ja hankalin malamin har ya sani a ‘Drama Club’ tare da amincewar mahaifina.
Daga lokacin da ka fara fim kawo i-yanzu za kayi kamar shekara nawa kana yi?
A kallah shekara takwas da fara dora min kyamara, amma a wasan dabe sama da shekara 25.
A wanne fim ka fara fito wa, kuma wanne rawa ka taka cikin fim din?
Fim dina na farko shi ne ‘Zuria Daya’ wanda kamfanin ‘FKD’ na Ali Nuhu suka shirya, kuma shi da kansa ya gayyace ni. Sannan fim din da na fara yin fice shi ne; ‘Dinyar Makaho’ na ‘Assmasan film production’ wato kamfani Sadik Sani Sadik a matsayin mahaifin Zainab Indomie.
Ko za ka iya tuna yawan adadin fina-finan da ka yi?
Gaskiya da wuya domin na yi fina-finai da dama kamar ‘Garba mai Walda, Allah Ya Hana Babu, Tafin Hannu, Fatake, ‘Ya Daga Allah, Labarina, Kisan Gilla, da dai sauransu.
Cikin fina-finan da ka yi wanne ne ya zamo bakandamiyarka wanda ka fi so ka fi kauna?
To a gaskiya dukkan fina-finai na ina sonsu, don ba zan iya ware wani guda daya na ce gashi ba, kamar yadda ba zan iya ware wani daga cikin ‘Ya’yana na nuna na fi sonsa ba
Ya ka Dauki fim a wajenka?
Ni na dauki fim a matsayin sana’a, don ba ni da wata sana’a da nake tunkaho da ita da ta zarce sana’ar fim.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da fim?
A gaskiya zuwa yanzu da muke tattaunawa babu wani kalubale da na fuskanta ban san ko zuwa gababa ba, saboda ajizanci irin na bani Adama.
To ya batun Nasarori fa?
Hakika na samu nasarori musamman yadda masoya suke ta dafifi wajen son mu kulla zumunci gami da addu’oin fatan alkhairi, wanda hakan shi ya ba da dama kike hira da ni don masoya su kara jin dadi kuma su nishadantu.
Ya za ka bambantawa masu karatu bambancin da ke tsakanin fina-finan baya da na yanzu?
To ai shi zamani riga ce kowa da irin tasa in ji masu karin magana, domin fina-finan baya sun karkata ne a kan yanayin da yake faruwa a wannan zamani, haka kuma fina-finan yanzu suna tafiya dai-dai da wannan zamanin da muke ciki.
Kana daya daga cikin masu taka rawa cikin shirin Labarina, shin kai ka zabi ka taka wannan rawar da kake takawa ko kuwa an ga dacewar hakan ya sa aka kira ka?
Ni ba ni na zaba ba kawai shi mai ba da umarni ne yake ganin zan dace kuma zan taka rawar gani shi ya sa ya kira ni.
Ya ka ji lokacin da aka dora ka a kan wannan rawar da za ka taka, kuma har ka kake takawa?
Gaskiyar magana kawai ji na yi zan iya kamantawa, kuma na yi iya kokari cikin taimakon Allah tare da gudun mawar abokan sa’a’a kuma cikin hukuncin Allah abin ya yi armashi.
Mafi yawan lokuta maganarka na canjawa cikin fina-finanka, misali kamar in aka hada fina-finai hudu ko uku za a ga duk maganar ka kusan iri daya, amma in aka duba wani fim din sai a ga maganar ba haka take ba, wai shin ita maganar sa ka ake ka canja ko kuwa kai ne da kanka idan ka ga dacewar hakan kake canja wa don ya kara armashi ko ya abin ya ke?
Hakikanin gaskiya na kan yi amfani da muryata dai-dai da yanayin shekarun da labari ya zo da shi.
To ya batun zaman gidan yari na cikin shirin labarina da kuma mukamin da ka rike a ciki, shin ka taba fim makamancin haka ko kuwa shi ne na farko da ka taka rawa irin hakan?
Wannan shi ne fim na farko da na fara yin irin wannan, batun mukami kuma da na samu a gidan yari hakan ya faru ne don irin tantirancin da nake aikatawa a waje kafin a kawo ni gidan gyaran hali.
Me ya fi birgeka a cikin fim din Labarina, wanne waje ne kuma wanda ka taka rawarsa ba ka ji dadin hakan ba?
Abin da ya fi burge ni shi ne yadda marubuta suka yi amfani da kwakwalwa wajen tsara labarin, sannan masu ba da umarni da suka zage wajen zakulo jaruman da suka dace kuma aka ajiye kowacce kwarya a gurbinta, kuma babu wata rawa da na taka da ban ji dadi ba saboda mai ba da umarni yana yabawa, wanda hakan ya sa ya yi min kyauta mai tsoka don jin dadin abin da na yi, amma wannan tsakanina da shi ne ba sai mai karatu ya ji kwakwaf ba.
Za mu ci gaba mako me zuwa, in sha Allahu.