A farkon makon nan ne gwamnatin Sin ta mikawa gwamnatin Najeriya sabuwar cibiyar binciken harkokin noma, wadda aka kammala ginin ta a garin Bwari dake kusa da birnin Abuja fadar mulkin kasar. Cibiyar dai daya ce daga ayyuka daban daban da kasar Sin ke tallafawa gudanarwa a Najeriya, a wani bangare na cika alkawarun da Sin din ta jima tana dauka, na agazawa abokan tafiyar ta wato kasashe masu tasowa.
Masana sun tabbatar da cewa, wannan cibiya ta bincike, za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa, da fadada ci gaban ayyukan noma a kasar mafi yawan jamaa a Afirka. Ko shakka babu, wannan cibiya za ta yi babban tasiri ga alummar Najeriya, musamman manoma, da hukumomin kasar masu nasaba da harkokin noma, da ma matasa wadanda a nan gaba za su samu zarafin shiga sanaar noma gadan gadan.
Mafiya yawa daga mazauna birane musamman matasa dake son fara sanaoi a Najeriya, ba su cika rungumar sanaar noma ba, duba da wahalhalun dake tattare da sanaar, ga kuma karancin dabarun zamani na gudanar da sanaar wanda kan haifar da karancin ribi, ko fuskantar asara yayin da ake gudanar da ita bisa salon gargajiya.
Sabuwar cibiyar dai na kunshe da abubuwa na binciken fasahohin zamani da ake amfani da su a harkar noma, da wuraren ba da horo ko samun kwarewar makamar aiki. Kaza lika ta kunshi kayan aiki na nazari domin saukaka noma a zamanance, ta yadda manazarta za su samu damar zakulo dabaru na sauya akalar ayyukan noma daga na gargajiya zuwa na zamani, da fito da dabarun bunkasa yawan hatsi da manoma za su iya nomawa a Najeriya, da ma fadada sassan noma da kiwo daban daban. Har ila yau, akwai dakunan gwaje gwaje, da madatsar ruwa, da cibiyar nune-nunen yadda ake sarrafa amfanin gona, da cibiyar samar da makamashi da sauran su.
Hakika wannan sabuwar cibiya, shaida ce dake nuni ga manyan nasarori da Sin tare da Najeriya suke samu, karkashin dadadden hadin gwiwa, da zumuncin dake tsakanin sassan biyu.
Tabbas, bisa abubuwan da aka tanada a wannan cibiya, yan Najeriya musamman manoma, za su ci babbar gajiya daga fasahohin zamani na bincike da gwaje gwaje, kuma cibiyar za ta ci gaba da zama wata alama, game da kyakkyawar dangantaka dake tsakanin Sin da Najeriya cikin tsawon lokaci. (Saminu Alhassan)