Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa, ba zai kara taimakawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba wajen isar da alfanun da ke tattare da sake fasalin tattalin arzikinta ga ‘yan Nijeriya.
Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Laraba, inda ya kara da cewa, ya yanke wannan shawarar ne saboda rashin halin ko in kula da gwamnatin ke yi masa.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbi Likita Tare Da Garkuwa Da Ma’aikatan Jinya A Wani Harin Asibiti A Katsina
- Ranar Tunawa Da Mazan Jiya: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu
Da yake jawabi a taron shekara-shekara na Gani Fawehinmi na 2025, da ya yi shuhura wajen gwagwarmayar kare hakkin dan’Adam, Sarkin ya bayyana cewa gwamnati ba ta da amintattun wakilai da za su iya bayyana sauye-sauyenta yadda ya kamata don haka ba zai cike wannan gurbi ba.
Sarki Sanusi II, sai dai ya bayyana cewa, “halin da muka tsinci kanmu ciki a yau, wani bangare ne na abinda shugabannin da suka gabata suka shuka na tsawon shekaru da dama da aka yi ana gudanar da harkokin tattalin arziki.
“An dade ana gargadin mutane shekaru da dama cewa, wannan hanyar ba mai dorewa ba ce, amma suka zabi son ra’ayinsu.
“Amma, idan gwamnati ta shirya don tattauna batun tattalin arziki, zan iya bayar da gudunmawata. A yanzu, na zo ne don karrama Cif Gani Fawehinmi,” in ji Sarki Sanusi.
Sarkin ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su koma kan tushensu na gaskiya da yin aiki tukuru.