Hukumar kididdiga ta kasar Ghana ta ce, tattalin arzikin Ghana ya bunkasa da kashi 5.7 cikin 100 a shekarar 2024, sakamakon gagarumin aikin masana’antu, a daidai lokacin da ake gudanar da sauye-sauyen tattalin arzikin kasar da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ke marawa baya.
Da yake jawabi ga manema labarai jiya litinin a Accra, babban birnin Ghana, Babban jami’in kididdiga na gwamnatin kasar, Samuel Kobina Annim, ya ce bunkasar tattalin arzikin ya kai kashi 2.6 cikin dari fiye da kashi 3.1 cikin dari da aka samu bayan da aka yi kwaskwarima a shekarar 2023.
Ya kara da cewa, “Duk da an samu tafiyar hawainiya a karuwar kashi 0.2 cikin 100 a rubu’i na hudu, bangaren masana’antu ya jagoranci ci gaban tattalin arzikin Ghana a shekarar 2024 tare da samun karuwar kashi 7.1 cikin 100, sakamakon ayyukan gine-gine da ma’adinai da fasa duwatsu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp