Fitaccen masanin tattalin arziki dan kasar Birtaniya John Ross, ya ce ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin ya karu da kaso 5.3 bisa dari a mizanin shekara, cikin rabin farko na shekarar nan ta 2025, wanda hakan ke nuni ga ingancin tushen tattalin arzikin kasar.
Ross, wanda ya bayyana hakan a baya-bayan nan, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce Sin ta wanzar da managarcin yanayin zuba jari, tana kuma kara fadada jarin da ake shigarwa a fannin bincike da samar da ci gaba, tare da ingiza daga matsayin fasahohi, wanda hakan ya haifar da managarcin yanayi na bunkasa tattalin arzikin kasar. A cewar shaihun malamin, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasa yadda ya kamata.
Bugu da kari, masanin ya ce, a matsayinta na kasa dake kan gaba wajen cinikayyar hajoji, Sin na ci gaba da ingiza manufar bude kofa mai inganci ga sassan kasa da kasa, tana kuma kara bude kofofin kasuwanninta ga duniya, da tsayawa tsayin daka wajen bunkasa dunkule tattalin arzikin duniya baki daya. Ya ce, ko shakka babu kasar Sin ta zamo babban ginshiki na ingiza dunkulewar duniya waje guda. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp