Wata kididdiga da aka fitar da dumi-duminta, ta nuna cewa, cikin watanni 8 na farkon bana, jimilar kayayyakin shige da fice na Sin, ta karu da kashi 3.5% bisa makamancin lokacin a bara. Lamarin ya sake nuna cewa, harkokin ciniki tsakanin Sin da kasashen waje, muhimmin bangare ne wajen inganta tattalin arzikin duniya, kuma babban ginshiki ne na karuwar tattalin arzikin duniya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian ne ya bayyana haka a yau Alhamis, yayin taron manema labarai na yau da kullum.
Game da shirin Mexico na kara harajin kwastam na kashi 50% kan motoci da sauran kayayyakin da ake shigar da su kasar, wadanda wasu kasashen Asiya ciki har da Sin suka kera, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya dade yana kira ga dunkulewar tattalin arzikin kasa da kasa mai fa’ida, kana yana adawa da duk wani nau’i na aiwatar da ra’ayin bangare daya da ba da kariya. Ya ce kasar Sin tana matukar mutunta bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Mexico, kuma tana fatan kasar Mexico za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen inganta farfadowar tattalin arzikin duniya da habakar cinikayya a duniya baki daya.
Haka zalika yayin taron, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan kasar Poland za ta dauki kwararan matakai masu inganci don tabbatar da aikin jiragen kasa na jigilar kayayyaki tsakanin Sin da Turai cikin aminci da lumana, da kiyaye daidaiton tsarin masana’antun samar da kayayyaki na kasa da kasa.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp