A lokacin hutun bikin Bazara da ya gabata, fitattun wuraren yawon shakatawa da gidajen sinima na kasar Sin sun cika makil da jama’a, fiye da makamancin lokaci na shekarar 2019. A cewar wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da CGTN da jami’ar Renmin da ke kasar Sin suka gudanar ta hanyar cibiyar jin ra’ayin jama’a ta kasa da kasa, sama da kashi 90 cikin 100 (wato 93.1%) na wadanda aka tattauna da su, sun yaba da karfin tattalin arzikin kasar Sin. Sun yi imanin cewa, jurewar da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki, da kuma karfin da take da shi, ba shakka, za su kara kuzari da karfin amincewa da tattalin arzikin duniya, wanda ke farfadowa sannu a hankali.
Kuri’ar ta shafi mutane 9,030 a fadin duniya, ciki har da mutane daga kasashen da suka ci gaba kamar kasashen Amurka, da Birtaniya, da Jamus da Australia, akwai kuma daga kasashe masu tasowa kamar Afirka ta Kudu, da Argentina, da Indonesia, da Pakistan, da Thailand, da Chile da Vietnam. (Ibrahim)