Fu Linghui, kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin ya bayyana a yau Laraba cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana samun farfadowa sannu a hankali, bayan da ya jure mummunan tasirin annobar COVID-19, inda manyan alamomi suka nuna kyakkyawan yanayin da tattalin arzikin ya samu a watan Mayu.
A yayin taron manema labarai, Fu ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar yana samun kyakkyawar farfadowa, sai dai ya yi gargadin cewa, har yanzu tattalin arzikin na fuskantar wahalhalu masu yawa gami da kalubaloli.
Ya ce, domin tinkarar yanayin da za a shiga a nan gaba, kasar Sin za ta tinkari aikin yaki da annobar tare da daidaita yanayin ci gaban tattalin arziki, da aiwatar da wasu karin matakai da manufofin raya tattalin arzikin domin samun ci gaba mai dorewa.(Ahmad)