Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, yayin da aka dauki sabbin matakan yaki da cutar COVID-19 a kasar Sin, babu shakka za a samu kyautatuwa kan tattalin arzikin Sin a sabuwar shekara, wanda zai kara samar da gudummawa ga raya tattalin arzikin duniya.
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da bayanan tattalin arzikin Sin na shekarar 2022 a kwanakin baya, inda kafofin watsa labaru na kasashen waje suka yi sharhi game da wannan batu cewa, yayin da ake kyautata matakan yaki da cutar COVID-19 a kasar Sin, za a samu saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin a bana.(Zainab)