An samu sabon ci gaba dangane da shirin EU na kara dora haraji kan motocin kasar Sin masu amfani da wutar lantarki a kwanan baya. A ranar 22 ga wata, ministan kasuwancin kasar Sin ya yi shawarwari da Valdis Dombrovskis, mataimakin shugabar hukumar kungiyar Tarayyar Turai wato EU kuma jami’in kula da harkokin ciniki, ta kafar bidiyo bisa gayyatar da aka yi masa, inda bangarorin 2 suka amince da fara tattaunawa kan binciken EU dangane da ko kasar Sin ta ba da tallafi kan motoci masu amfani da wutar lantarki da ake sayarwa zuwa ketare ko a’a. Lamarin da ya nuna cewa, Sin da EU suna da niyyar daidaita matsalar cinikayya ta hanyar tattaunawa, wadda ke kokarin kawo illa ga hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.
A shekarun baya-bayan nan, EU kan ta da rikicin cinikayya a tsakaninta da Sin. Tun daga farkon bana, EU ta fito da matakai guda 31 na sanya kaidi kan yin ciniki da zuba jari a kasar Sin, lamarin da ya rura wutar rikicin cinikayya a tsakanin bangarorin 2. An fahimci sosai cewa, EU tana kawo tsaiko ga yin takara cikin adalci, da ba da kariyar ciniki, da takaita karfin ‘yan takara, da dakile ci gaban masana’antun sabbin makamashi na kasar Sin, da hana daga matsayin masana’antun kasar Sin, da kuma nuna goyon baya ga kawarta wato kasar Amurka.
Ba da kariya kan cinikayya, ba zai kiyaye kwarewar yin takara ba. Masana’antun sabbin makamashin kasar Sin na samun ci gaba duk da takara mai zafi a kasuwa, a maimakon samun tallafin gwamnati da kuma yin takara ba cikin adalci ba. Kasar Sin na fatan EU za ta yi watsi da akidar tunani da kuma riba ta gajeren lokaci, ta dauki matakai masu dacewa, ta yi tattaunawa da Sin don samun sakamakon da dukkansu za su amince da shi, kuma zai dace da muradunsu duka. (Tasallah Yuan)