TASKIRA, shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. A makon jiya mun kawo muku kashi na farko na babban batun da shafin yake tattaunawa a kai game da abin da ya shafi bashi, duba da yadda wasu mutanen ke daukar bashi ba komai ba, yayin da za su ci bashin mutane kuma su ki biya da gangan, wanda hakan ke iya zamowa zumunci ya tarwatse ta dalilin bashin. A halin yanzu ga kashi na biyu na wannan batun, inda wasu daga cikin ma’abota shafin suka tofa albarkacin bakinsu game da wannan batu;
Ko me yake janyo cin bashi? Me ne ne amfani ko rashin amfanin cin bashi? Wanne irin matsaloli cin bashi ke haifarwa? Wadanne irin matsaloli ne ke sakawa a ci bashi?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aisha Mahmud, Jihar Katsina:
Matsi ke kawo cin bashi, amfanin ta shi ne biyan bukatar a ta kokari, rashin amfaninta kuma shi ne; idan ana wulakantaka akan bashin da ka ciwo. Ta na haifar da cin mutunci, kaskantarwa musamman idan ba ka biya a kan lokaci ba. Kamar matsalar rashin lafiya da rashin abinci.. Bashi dai ba ta haifar da kwanciyar hankali don haka a daina karba marasa biyan bashi kuma gobe ai ba wanda zai ba su.
Sunana Tijjani Abubakar Atiku, Hadejia Jigawa:
Mutane suna cin bashi ne saboda biyan wata bukata na kudi, ko kudi yayi musu kadan kuma suna da bukatar kudin dan cinma wani abu na yau da kullum. Kamar yadda komai yake da amfani da rashin amfani, bashi na da amfani sosai wurin biya wa mutum bukatar sa wanda ya zama dole a gare shi, babu wanda zai ce bai taba cin bashi ba ko Dangote daya fi kowa kudi a Africa sai da ya ciwo bashi dan ya kammala refinerinsa dake Lagos, rashin amfaninsa yana janyo a raina mutum musamman mutanen dake cin bashi ba sa biya. Cin bashi na janyo matsaloli da dama, daga ciki akwai haddasa gaba tsakanin mutane, mutum ne ya ciwo bashi yanada kudin biya amma sai ya ki biya, bashi yana janyo raini, bashi yana janyo yanke zumunta da sauransu. Akwai yanayin dake saka mutum dole ya ciwo bashi musamman aure, kasuwanci da noma. Wato shi bashi abu ne mai hatsarin gaske, rashin biyansa yakan kai mutum ga halaka. A musulunce rashin biyan bashi yakan janyo mutum ya hadu da fushin Ubangiji. Shawarar da zan bawa masu cin bashi ita ce; abu in bai zama dole a gare ka/ki ba to kar ka ci bashi dan ka biya wannan bukatar, sannan masu cin bashi su ki biya wannan ba dabi’a bace ta kwarai, a gyara.
Sunana Khadeejah Ibraheem Bello, daga Abuja:
Abubuwan da ke janyo cin bashi na da yawa, amma yawanci rashi ke jawo wa. Gaskiya cin bashi baida wani amfani, hasali ma sai ya jawo wa mutum raini da cin fuska. Yana haifar da mutuwar zuwa da tsana a cikin al’umma Yawanci rashi ke jawo wa. Şu nemi sana’ar yi komai kankantarta, kuma şu daina son zuciya da mutuwar zuciya.
Sunana Abdullahi Dahiru Matazu:
Babban dalilin da yake kawo wa ka ga mutum ya ci ba shi shi ne; idan muka yi duba da halin da muke ciki ba yanzu ba har lokutun da suka shude a baya shi ne; matsala. Cin bashi ba shi da wani amfani a wannan rayuwar, hasali ma cin bashi baida amfani sai dai rashin amfani, amma ya zama dole ne a wajen wasu. Matsalar da cin bashi ya ke haifar wa za ka ci bashi a wajen yaron da ka haife shi amma duba wannan, koda yaushe kana kokari domin ka ga ka biya shi amma abun ya ci tura, shi kuma ya samu damar raina ka da kuma ci ma mutunci. Matsalar cin bashi iyayenmu su ne; suke dawainiyya da mu, saboda haka sune suke cin bashi domin wasu yaransu ba su da lafiya, wasu kuma babu abinci dama sauran matsalolin rayuwa. Shawara ita ce; tun daga lokacin da mutumin ya baka bashi to ya gama rufa maka asirin duniya, kawai idan Allah ya baka kayi hakuri ka biya shi, ko kuma lokacin da ku ka dauka ya yi baka samu kudin ba to ka je ka bashi hakuri shi ne kawai.
Sunana Salma Ahmad, Jihar Bauchi:
Duk wanda ya ji sunan bashi ya san ba abu ne da za a yi alfahari da shi ba, sai dan ya zama dole mutum ya nema, sai dai wasu suna karba ne kawai dan cimma burukansu na rayuwa dan ganin sun saka abin da ba su da shi, ko sun mallaki abin da wane ya mallaka ta karfin tsiya, wanda kuma hakan ke saka wa su kasa biyan bashin da suka daukarwa kansu. Rashin ci da sha da samun n karatu ke saka wa a ci bashin dole, ko kuma neman jari dan samun mafitar rayuwa. Shawarata ga masu cin bashi ba tare da sun buya ba su daina, domin cin bashi yana hana kwanciyar kabari.
Bashi kawai yana nufin adadin kudi ko wani abu da wani mutum ko mahaluki ke bin wani, yana iya zama ta hanyar kudin aro, kaya, ko ayyuka. Manufa ko muhimmancin bashi ya bambanta dangane da muhallin. Ga daidaikun mutane, ana iya amfani da bashi don ba da kudin sayayya, muhimmanci kamar gida ko ilimi. A cikin duniyar kasuwanci ana iya amfani da bashi don tallafawa, fadadawa, ko saka hannun jari a sabbin ayyuka. Matsalolin gama gari masu alaka da basussuka sun hada da damuwa ta kudi, wahalar biyan kudi, yawan kudin ruwa, da yuwuwar lalacewar kima. Yanada mahimmanci a sarrafa bashi cikin gaskiya don guje wa wadannan abubuwan. Duk da yake bashi na iya zama kayan aiki mai amfani, akwai hadari a cin bashi, har ma ida mutum ya ci bashin da ba zai iya biya ba bashi da yawa na iya haifar da rashin kwanciyar hankali. Ga wadanda basu da tabbacin karbar bashi, shawarata ita ce; su yi nazari sosai kan halin da suke ciki na kudi, su tsara kasafin kudi, su yi la’akari da wasu hanyoyi. Yana da mahimmanci a fahimci sharuda da sharudan kowanne yarjejeniyar bashi su kuma tabbatar da cewa ta yi daidai da manufofin na kudi. Neman jagora daga mai bada shawara kan harkokin kudi na iya bada haske mai mahimmanci. Ka tuna, yana da kyau ko yaushe ka kasance mai hankali kuma ka yanke shawara mai kyau idan ya zo ga bashi.
Sunana Kabir Muhammad Sani, Jihar Kaduna Road:
Bukata ke janyo cin bashi, kuma hakan ya halatta amma da niyyar biya, amfaninsa shi ne; samun biyan bukatar a lokacin matsuwa, damuwa duk da halaccin sa, domin manzon tsira ya kira shi da kaskanci da ranar bakin ciki da daddare. Matsalar da take wajibi wadda dole ne a yi ta ko ta ya ya, kamar abinci ko magani da makamantansu. Shawara su yi ta addu’a ubangiji ya yassare musu abun biya da kuma ikon biyan, sannan duk abin da ba dole ba kada su ci bashi dominsa.
Sunana Nasir Mahmud Yahya daga Adamawa:
Matsaloli na rayuwa, abin da ke janyo cin bashi da kuma amfaninsa shi ne; Akwai salama da kai idan ba bashi akan mutum, Rashin kirki, rashin kwanciyar hankali, rashin kulawa daga wadanda aka ciwo bashinsu. Rahin lafiya, rashin abinci. Shawara a rika hakuri da juna.