A halin yanzu dai tawagar da gwamnatin tarayya ta tura domin halartar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata ta isa garin Madina na ƙasar Saudiyya.
Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai bai wa Ministan yaɗa labarai shawara, Rabiu Ibrahim, ta bayyana cewa tawagar ta bar Nijeriya a yammacin jiya Lahadi, sannan ta isa Madina da sanyin-safiyar yau Litini.
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kan Al’ummar Benuwe, Sun Kashe ‘Yansanda 4
- Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba
Sanarwar ta Rabiu ta kuma bayyana cewa tawagar gwamnatin tarayyar tana ƙarƙashin jagorancin Ministan tsaro, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata.
Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad.
Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini.
Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa a Asabacin da ta gabata, yana mai shekaru 94.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp