• English
  • Business News
Monday, August 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

by Sulaiman
2 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kashi na 34 na tawagar likitocin kasar Sin da ke birnin Zanzibar na kasar Tanzaniya, sun gudanar da ayyukan kiwon lafiya kyauta ga marayu da ma’aikatan gidan marayun fiye da 200 a ranar Asabar da ta gabata a karkashin wani shirin ba da kulawa da aka yi wa lakabin “Angle’s Care Initiative” a Turance.

Likitocin kasar Sin daga sassa daban-daban da suka hada da kwararru a kan likitancin cikin jikin manya, da tiyata, da likitancin mata, da na ido, da na kunne da makogoro, da na hakora, sun gudanar da gwaje-gwaje na zahiri ga yara da ma’aikatan gidan na marayu.

  • Ƴansanda Sun Gano  Ƙarin Bama-Bamai 9 Da Basu Fashe Ba A Kano
  • Binciken CGTN: Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Kasa Da Kasa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Amurka Kan Iran

Tawagar likitocin kasar Sin ta yi cikakken bayani game da gwaje-gwajen da ta gudanar tare da bai wa ma’aikatan gidan marayun umarni kan yadda ya kamata a rika bibiyar hanyoyin kulawa, da kuma ka’idojin magani ga wadanda ke fama da rashin lafiya. Har ila yau, bayan kammala binciken kiwon lafiyar, ‘yan tawagar sun raba kyaututtuka da suka hada da kayan makaranta, da kwallayen kafa, da kayan ciye-ciye ga yara.

Jami’ar tuntuba ta ma’aikatar kiwon lafiya ta Zanzibar, Mariam Khalfan ta nuna matukar godiyarta ga tawagar likitocin ta kasar Sin bisa taimakon da take bai wa Zanzibar.

Mariam ta kara da cewa, likitocin kasar Sin sun dadada ran marayun Zanzibar tare da kara musu kwarin gwiwa, inda suka kulla sada zumunci da ke ci gaba da karfafa dangantaka a tsakanin bangarorin biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Labarai Masu Nasaba

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027

Next Post

Gargaɗin Amurka: Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja

Related

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro
Daga Birnin Sin

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

2 hours ago
Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK
Daga Birnin Sin

Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK

21 hours ago
Sin Ta Gudanar Da Gwajin Farko Na Gagarumin Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Dakarun Japan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gudanar Da Gwajin Farko Na Gagarumin Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Dakarun Japan

22 hours ago
Sin Na Gaggauta Gina Tsarin Tattalin Arziki Mai Kiyaye Muhallin Halittu
Daga Birnin Sin

Sin Na Gaggauta Gina Tsarin Tattalin Arziki Mai Kiyaye Muhallin Halittu

23 hours ago
Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan
Daga Birnin Sin

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

2 days ago
Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Daga Birnin Sin

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

2 days ago
Next Post
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

Gargaɗin Amurka: Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC

Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC

August 11, 2025
Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

August 11, 2025
Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara

Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara

August 11, 2025
Borno

‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno

August 11, 2025
Yajin aiki

Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki A Taraba

August 11, 2025
Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19

Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19

August 11, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

August 11, 2025
Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

August 10, 2025
Ƴansanda Sun Kama Makashin Wani Ɗan Jarida A Abuja Bayan Shekara Ɗaya

Ƴansanda Sun Kama Makashin Wani Ɗan Jarida A Abuja Bayan Shekara Ɗaya

August 10, 2025
Fa’ida Da Muhimmancin Tattalin Lokaci Ga Ɗan’adam

Fa’ida Da Muhimmancin Tattalin Lokaci Ga Ɗan’adam

August 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.