ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gargaɗin Amurka: Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja

by Sulaiman
1 year ago
Abuja

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin cewa Babban Birnin Tarayya Abuja yana da tsaro ga mazauna cikin sa da baƙi da kuma jakadun ƙasashen waje.

Wannan tabbacin na zuwa ne bayan da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya fitar da wata sabuwar sanarwa kan tsaro, inda ya hana tafiye-tafiyen ma’aikatan sa da iyalan su zuwa wuraren soja ko wasu gine-ginen gwamnati a Abuja, in ba don ayyuka na hukuma ba.

ADVERTISEMENT
  • An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027
  • Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin kowane ofishin jakadanci na fitar da irin wannan gargaɗi ga ‘yan ƙasar sa, sai dai ya jaddada cewa babu wani haɗari na kai-tsaye a Abuja.

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.”

Ya bayyana cewa hukumomin tsaro a Nijeriya suna aiki tuƙuru dare da rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya ƙara da cewa tsarin tsaro a Abuja yana aiki yadda ya kamata tare da nasarori masu yawa wajen gano duk wata barazana da kuma daƙile ta kafin ta faru.

Ministan ya ƙara da cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ba ya nuni da wata barazana kai-tsaye ga Abuja, illa ya dogara ne da al’amuran tsaro na duniya gaba ɗaya.

Ya ce: “Mun fahimci cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ya ta’allaƙa ne da wasu abubuwan da ke faruwa a duniya gaba ɗaya, ba wai yana nuna wata barazana kai-tsaye ko ta gaggawa a cikin Babban Birnin Tarayya ba.

“Sai dai muna sake jaddadawa ga dukkan ofisoshin jakadanci, da masu zuba jari da abokan cigaba, da jama’a gaba ɗaya cewa babu wani dalilin fargaba.”

Ya kuma bayyana ƙudirin gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a birnin tarayya, yana mai cewa: “Gwamnatin Tarayya tana son sake jaddada ƙudirin ta na kare lafiyar duk mazauna ƙasar nan tare da ci gaba da tabbatar da martabar Abuja a matsayin ɗaya daga cikin manyan biranen da suka fi tsaro a duniya.”

Daga ƙarshe, ya buƙaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba, tare da yin taka-tsantsan da kuma bayar da rahoto kan duk wani abu da suka ga ya ɗaure masu kai ga jami’an tsaro mafi kusa.

Abuja
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.