Tawagar likitocin Sin ta 23 da ke kasar Rwanda, ta ba da gudummawar kayayyakin jinya ga asibitin Masaka da ke gundumar Kicukiro a Kigali, babban birnin kasar.
Tawagar ta gabatar da kayayyakin jinya iri daban-daban ga asibitin jiya Litinin, wadanda suka hada sinadarin wanke hannu, da kayan aikin jinyar hakora, da tabaran likitoci, da kayan aikin yau da kullum, da teburin yin tiyata mai aiki da wutar lantarki.
Da yake karbar tallafin a asibitin Masaka, babban darekta Jean Damascene Hanyurwimfura, ya bayyana jin dadinsa ga tawagar likitocin kasar Sin, bisa taimakon kayayyakin kiwon lafiya da suke baiwa asibitin. (Mai fassarawa: Ibrahim)