Bayan aukuwar wata girgizar kasa mai karfin gaske jiya Juma’a a kasar, da sanyin safiyar yau Asabar, agogon Myanmar din, tawagar ma’aikatan ceto ta lardin Yunnan na kasar Sin, mai mambobi 37, ta isa birnin Yangon na kasar. Tawagar wadda ta kasance tawagar ceto ta kasa da kasa ta farko da ta isa Myanmar, na dauke da na’urorin agajin gaggawa guda 112, ciki har da na’urorin tantance mai rai, da na gargadin girgizar kasa, da na’urorin sadarwa masu amfani da tauraron dan adam, da na’urori masu tashi sama.
Kafin haka, wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta damu matuka da bala’in girgizar kasar da ta afku a kasar Myanmar, inda ya jajenta wa al’ummar kasar. Ya ce kasar Sin tana son ba da agajin gaggawa da taimakon jin kai ga yankunan da bala’in ya rutsa da su gwargwadon karfinta, kuma bisa bukatun kasar Myanmar. Bugu da kari, ya ce Sinawa za su kasance tare da al’ummar Myanmar wajen yaki da bala’in da kuma shawo kan matsalolin da ake fuskanta.
- Shugaba Xi Ya Jajantawa Shugaban Myanmar Game Da Girgizar Kasar Da Ta Auku
- Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah
Ban da haka, kasar Sin ta yanke shawarar samar wa Myanmar tallafin jin kai na yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 13.9, domin taimakawa wajen saukaka radadin ibtila’in girgizar kasa da ta aukawa kasar. Kakakin hukumar raya kasashe ta kasar Sin Li Ming ne ya bayyana haka a yau Asabar. Ya kara da cewa, bisa bukatar gwamnatin Myanmar, Sin za ta tura tawagogi 2 na ma’aikatan ceto tare da samar da tantuna da barguna da kayayyakin kiwon lafiya na gaggawa da abinci da ruwan sha, wadanda su ake mutukar bukata a yankunan da ibtila’in ya shafa.
Da tsakar ranar jiya Juma’a, agogon kasar Myanmar, girgizar kasa mai karfin maki 7.9 ta afku a tsakiyar kasar, bala’in da ya sanya dimbin yankunan kasar shiga cikin dokar ta-baci. A cewar kafofin yada labaru na Myanmar, bala’in ya riga ya haddasa mutuwar mutane 1002 tare da jikkata wasu 2376 a cikin kasar, kuma adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa. (Bello Wang/Fa’iza Muhammad Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp