Mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri a daren 9 ga watan Satumba, sakamakon rugujewar madatsar ruwa ta Alau, ta yi sanadiyyar raba dubun dubatar mutane da muhallansu.
Shugabannin hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, tare da daraktocin ƙasa na ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya sun ziyarci Maiduguri a yau.
- Ambaliyar Ruwan Maiduguri Ta Shafi Mutane Sama Da Miliyan 1 – Gwamnati
- Ambaliya: Uwargidan Gwamnan Yobe Ta Janjanta Wa Al’ummar Maiduguri
Sun gana da mutanen da abin ya shafa da jami’an gwamnati a babban birnin jihar Borno. Kana sun bayyana yunƙurin su na tallafawa ƙoƙarin Gwamnati ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattara ƙarin agaji don ɗaukar matakan ceton rayuka.
Kimanin mutane 300,000 ne cibiyar bayar da agajin gaggawa ta Gwamnatin Jihar Borno ta yi wa rijista a wuraren da aka tsugunar da su musamman a ƙananan hukumomin cikin birnin Maiduguri (MMC), da Jere da kuma Konduga.
Mutane da dama da ambaliyar ta shafa, waɗanda aka ruwaito sun kasance mafi muni cikin shekaru sama 30 da suka gabata, suna da buƙatu na jin ƙai kafin aukuwar ambaliyar, inda tashe-tashen hankula da rashin tsaro suka rasa matsugunansu a lokuta da dama, kuma a yanzu suna cikin mawuyacin hali.
A ƙarƙashin jagorancin babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall, manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun gana da Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, sun jajanta wa gwamnati da al’ummar Borno sakamakon asarar rayuka da ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Jami’an sun ziyarci makarantar firamare ta Asheik Jarma da kuma sansanonin Yerwa GGSS, biyu daga cikin fiye da 25 wuraren da aka tsugunar da ‘yan gudun hijirar na wani ɗan lokaci. “Na ga irin ɓarnar da ambaliyar ta haifar, da kuma rugujewar gidaje, da wuraren kasuwanci, da ababen more rayuwa. Na kuma ga yadda al’ummomin da abin ya shafa ke shan wahala,” in ji Mista Fall.
Ya ce yadda ambaliyar ruwa ta yaɗu a MMC da Jere na buƙatar mayar da martani ga Majalisar Ɗinkin Duniya da abokan hulɗa, don tallafawa ƙoƙarin Gwamnati. “Mutanen da ambaliyar ta shafa suna fuskantar rikici a cikin wani rikici tare da ambaliya a lokacin da ake fama da matsanancin rashin abinci da rashin abinci mai gina jiki,” in ji shi.
A duk faɗin Najeriya, ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da hekta 125,000 a daidai lokacin da mutane miliyan 32 ke fuskantar ƙarancin abinci a ƙasar.
A jihohin Borno, Adamawa da Yobe kaɗai, mutane miliyan 4.8 ne ke fuskantar matsananciyar ƙarancin abinci, yayin da rayukan yara 230,000 ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.