Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, wata tawagar manyan wakilan ofisoshin jakadancin kasashe 14, da suka hada da Brazil, da Iran, da Indonesia, da Pakistan, da Ecuador da Senegal, ta isa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta dake arewa maso yammacin kasar Sin, tsakanin ranaikun 24 zuwa 28 ga watan Afirilun nan.
Manyan jami’an jakadancin na kasashe 14, dake zaune a sassa daban daban na biranen kasar Sin, sun ziyarci biranen Urumqi, da Kashgar, Turpan, da wasu karin wurare a jihar ta Xinjiang, inda suka ganewa idanun su ainihin halin zamantakewa da ci gaban tattalin arzikin yankin.
Da suke tsokaci game da abubuwan da suka gani, jami’an sun ce jihar Xinjiang ta samu gagarumin ci gaba, kuma daukacin kabilun jihar na rayuwa cikin yanayi na lumana da farin ciki.
Sun kuma ce karairayin da wasu kafafen watsa labarai na yammacin duniya ke yadawa game da Xinjiang, sun yi hannun riga da ainihin gaskiyar abun dake faruwa. (Saminu Alhassan)