Bisa sanarwar da ma’aikatar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta bayar, tun daga yau wato ranar 6 ga wannan wata, Sinawa masu tashi zuwa kasashen waje guda 20 domin yawon shakatawa, za su sake kasancewa cikin tawagogi. Don haka, yau da sassafe, wasu tawagogin yawon shakatawa da za su je kasar daular Larabawa da sauran kasashen waje, suka tashi daga filin jiragen sama na Baiyun na birnin Guangzhou.
An ce, a yau, tawagogin yawon shakatawa guda shida dake kunshe da mutane kimanin 160 ne suka tafi kasashen waje daga birnin Guangzhou.
Game da wuraren yawon shakatawa da Sinawa suke so, bisa dawo da hanyoyi jiragen sama na kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Sin da sauran kasashe, a halin yanzu a birnin Guangzhou, an riga an gabatar da shirye-shiryen yawon shakatawa zuwa kasashen waje, cikinsu har da Thailand, da Singapore, da Malaysia, da daular Larabawa da sauransu. (Zainab)